Firaministan Sin Li Qiang, ya halarci, tare da gabatar da jawabi, a bikin bude baje kolin Sin da ASEAN karo na 20, da dandalin kasuwanci da zuba jari na Sin da ASEAN, wanda aka kaddamar a Lahadin nan a birnin Nanning dake kudancin kasar Sin.
Cikin jawabin da ya gabatar, Li Qiang ya ce alakar Sin da kungiyar ASEAN, ta cimma manyan nasarori, ta kuma zama tsayayyen tsari na bunkasa hadin gwiwar kasashen yankin Asiya da tekun Fasifik.
Ya ce domin cimma nasarar samar da makoma mai haske, ya dace a dora muhimmanci a sassan 4. Na farko a kara zurfafa dabarun hade tunani wuri guda. Na biyu a dinke tushen amincewa juna. Sai na uku wato zurfafa dinke dankon bukatun juna waje guda. Kana na hudu a kara ingiza manufar rungumar juna da budaddiyar zuciya.
A cewar firaministan na Sin, kasar sa za ta ingiza shawarar nan ta ziri daya da hanya daya, ta yadda za ta yi daidai da sauran kudurorin raya kasashen duniya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)