A yau da safe, firaministan kasar Sin Li Qiang ya halarci zama na uku na taron koli na shugabannin kasashen kungiyar G20 karo na 18 tare da gabatar da jawabi a birnin New Delhi dake kasar Indiya.
A cikin jawabinsa, Li Qiang ya bayyana cewa, ci gaban da ake samu a duniya a halin yanzu yana cikin mawuyacin hali mai sarkakiya kuma yana sauyawa cikin sauri, bisa wannan yanayi, ya kamata a karfafa imani ga kyautata fatanmu a nan gaba, da hangen nesa, da yin taka tsan-tsan da tinkarar kalubale.
Li Qiang ya yi nuni da cewa, ya kamata membobin kungiyar G20 su taka rawar gani, da aiwatar da ayyukansu yadda ya kamata. A halin yanzu, batun da yake daukar hankali, shi ne aikin samun bunkasuwa. Ya kamata a mai da aikin samun bunkasuwa a matsayin muhimmin matsayi bisa manyan tsare-satre, da kafa tsarin hadin gwiwa mai inganci, da daukar kwararan matakai don taimakawa kasashe masu tasowa wajen tinkarar kalubalen ci gaba da suka hada da yaki da talauci, da tattara kudi, da sauyin yanayi, da samar da abinci, da makamashi da sauransu.
A tsakar ranar 10 ga wata agogon wurin ne, aka rufe taron koli na shugabannin kasashen kungiyar G20 karo na 18, inda aka zartas da “Sanarwar shugabannin G20 na New Delhi”. (Zainab)