Firaministan kasar Sin Li Qiang ya isa Singapore a yau Asabar don ziyarar aiki a kasar bisa gayyatar firaministan Singapore Lawrence Wong.
Li ya bayyana cewa, a cikin shekaru 35 da suka gabata tun bayan kafa huldar diflomasiyya, dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ta ci gaba da kasancewa mai kyau da samun ci gaba, tare da zurfafa amincewa da juna a siyasance, da hadin gwiwa mai amfani da kuma mu’amala ta kut-da-kut tsakanin mutanensu, wanda ya kafa misali don koyo tare da hadin gwiwar samun nasara ga kowane bangare a tsakanin kasashe.
Ya kara da cewa, kasar Sin tana son yin aiki tare da Singapore don karfafa daidaita dabarun ci gaba, da fadada hadin gwiwa mai amfani ga dukkan bangarorin biyu, da ci gaba da yin aiki tare a cikin shirin zamanantarwa, da kuma bayar da gudummawa sosai wajen tabbatar da hadin gwiwa tsakanin bangarori daban-daban da kuma bunkasa ci gaba na bai-daya a yankin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)












