Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya bukaci a yi kokarin karfafa ilimin sana’o’in hannu da samar da kwararrun ma’aikata domin cimma bukatun ci gaban tattalin arziki da zamantakewar kasar.
Yayin ziyararsa a Shanghai domin nazarin ayyukan da birnin ke yi a fannin raya ilimin sana’o’in hannu da samar da kwararrun ma’aikata, Li Qiang ya ce samar da kwararrun ma’aikata za ta bayar da goyon baya mai karfi ga samun ci gaba mai inganci da ma ingantacciyar rayuwa.
- CIIE Ya Tabbatar Da Matsayin Kasar Sin A Tattalin Arzikin Duniya
- Ƴansanda Sun Kama Ƴan Ƙasar Waje 130, Da Ake Zargi Da Sata Ta Yanar Gizo
Da ya ziyarci kwalejin nazarin fasahohi da sana’o’in hannu ta Nanhu, Li Qiang ya ce akwai bukatar zurfafa dunkulewar harkokin sana’o’i da ilimi da kuma samun hadin gwiwa tsakanin kwalejoji da kamfanoni, domin inganta tsara fannonin karatu bisa bukatun al’umma da na raya sana’o’i da karfafa hanyoyin koyarwa a aikace, yana mai cewa, ana bukatar karin kwararrun malamai domin su kirkiro sabbin dabaru da salon koyarwa.
Da yake tsokaci game da ci gaba da karuwar bukatun kula da tsoffi da yara da kiwon lafiya, Li Qiang ya bukaci a karfafa kokarin horar da kwararrun ma’aikata a wadannan fannoni. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)