Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya jaddada bukatar karfafa rawar da bangaren hada-hadar kudade na kasar ke takawa wajen daidaita bangarorin tattalin arziki da inganta hidimomin hada-hadar kudi, domin tabbatar da tattalin arzikin ya ci gaba da gudana kan mataki mafi dacewa.
Li Keqiang ya bayyana haka ne yayin ziyarar da ya kai babban bankin kasar da hukumar kula da musayar kudaden ketare ta kasar (SAFE) a jiya, inda ya jagoranci wani taron karawa juna sani.
Da yake tattaunawa da jami’ai a cibiyar zuba jari ta hukumar SAFE, firaministan ya ce yayin da Sin ta fuskanci matsaloli daga waje a shekarun baya-bayan nan, asusun ajiyarta na kudaden ketare ya zarce dala triliyan 3, kuma farashin musayar takardar kudin yuan bai gamu da wata matsala ba, inda ya ci gaba da bayar da goyon baya mai karfi ga cinikayya da ketare da bangaren kudi na kasar da ma na tattalin arziki.
Ya kara da cewa, sabon garambawul da aka yi wa bangaren kudi ya karfafa bunkasar tattalin arzikin kasar. Yana mai cewa tattalin arziki mai karfi ne kadai zai iya samar da bangaren kudi mai aminci, kuma sai bangren kudi na da karfi da daidaito ne za a samu ci gaban tattalin arziki. (Fa’zia Mustapha)