Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya gudanar da taron tattaunawa da wakilan baki kwararru wadanda ke aiki a kasar da wadanda suka samu lambar yabo ta Abota ta Gwamnatin Sin.
Yayin taron wanda ya gudana jiya Lahadi, a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, Li Qiang ya kuma mika gaisuwar sabuwar shekarar gargajiya ta al’ummar Sinawa da fatan alheri ga bakin kwararru, ya kuma godewa goyon baya da kulawar da suka dade suna bayarwa ga kokarin Sin na zamanantar da kanta. Har ila yau, ya saurari ra’ayoyi da shawarwarinsu kan ayyukan gwamnatin Sin da manufarta ta gyare-gyare da neman ci gaba.
- Shugaba Xi Ya Yaba Da Ci Gaban Kasar Sin Duk Da Kalubalen Da Aka Fuskanta A Shekarar Dragon
- Ana Shirin Kiranye Ga Ɗan Majalisar Da Ya Bar Kwankwasiyya
Kwararrun wadanda suka hada da ’yan kasashen Birtaniya da Poland da Mali da Romania da Jamus da Pakistan, sun gabatar da jawabai kan maudu’i daban daban, kamar na kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da hadin gwiwar cinikayya da tattalin arziki da musayar al’adu da kuma musaya tsakanin jama’a da raya kwararru da ma cudanyar kasa da kasa.
Mataimakin firaminista Ding Xuexiang ma ya halarci taron. (Fa’iza Mustapha)