Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya yi kira ga aiwatar da matakai da za su zamo misali na bude kofa, da raya hadin gwiwa, da dunkule mabanbantan wayewar kai tsakanin Sin da ASEAN da GCC.
Li Qiang, ya bayyana hakan ne a Talatar nan, cikin jawabinsa ga bikin kaddamar da dandalin Sin da ASEAN da GCC, wanda aka bude a birnin Kuala Lumpur fadar mulkin kasar Malaysia.
Li, ya kuma yi kira ga sassan uku da su samar da wani salo na yin komai a bude tsakanin shiyyoyi, duba da cewa adadin al’ummunsu, da darajar tattalin arzikin da suke da shi ya kai rubu’in na duniya baki daya. Don haka dinkewar kasuwannin sassan 3, zai samar da babban fage na bunkasa da muhimmin tasirin da ake fata. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp