Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya yi kira ga kasashe membobin kungiyar BRICS, da su zamo ginshikan bunkasa sauyi ga tsarin jagorancin duniya.
Li ya yi kiran ne a jiya Lahadi, cikin jawabinsa a yayin bude taron kungiyar ta BRICS karo na 17, bisa taken “Zaman lafiya da tsaro da sauyi ga tsarin jagorancin duniya”, inda ya ce kamata ya yi membobin kungiyar su ba da gudummawa ga manufofin wanzar da zaman lafiya da lumana a duniya, kana su ingiza salon warware rigingimu ta hanyoyi na maslaha.
- Namadi Sambo Ya Yaba Wa Gwamna Abba Yusuf Kan Bunƙasa Ɓangaren Ilimi Da Gine-Gine A Kano
- Sojoji Sun Fatattaki Ƴan Bindigar Da Suka Zo Sace Wani Ɗan China
Ya ce ya dace kasashe membobin BRICS su mayar da hankali ga matakan samar da ci gaba, da bunkasar kuzarin raya tattalin arziki, kana su yi aiki tukuru wajen ingiza hadin gwiwar neman ci gaba, da habaka sabbin fannoni.
Firaministan na Sin ya kara da cewa, a bana kasarsa za ta kafa cibiyar nazari ta Sin da BRICS, wadda za ta mayar da hankali ga sabbin karfin samar da hajoji masu inganci, kana za ta samar da guraben karatu domin gajiyar kasashe membobin BRICS, da nufin bunkasa kyankyashe matasa masu kwarewa a fannoni daban daban na masana’antu da sadarwa.
Shugabannin kasashe membobin BRICS sun hallarci taron, ciki har da mai masaukin baki shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva. An kuma amince da sanarwar Rio de Janeiro ta taron karo na 17. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp