Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya yi kira ga kasashe membobin kungiyar G20 da su rungumi juna, su ingiza tsarin cinikayya cikin ‘yanci, da gina budadden salon raya tattalin arzikin duniya, a gabar da farfadowar tattalin arzikin duniya ke tafiyar hawainiya.
Li, ya bayyana hakan ne cikin jawabinsa a zama na farko na taron G20 karo na 20, dake gudana a birnin Johannesburg na Afirka ta kudu. Zaman dai ya mayar da hankali ne ga dunkule dukkanin sassa, da wanzar da ci gaban tattalin arziki, ya kuma gudana karkashin jagorancin shugaban Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa.
Firaministan na Sin ya ce tattalin arzikin duniya ya sake gamuwa da manyan kalubale, ciki har da farfadowar daukar matakai daga bangare guda, da kariyar cinikayya, da ma karuwar shingayen cinikayya da fito-na-fito. Daga nan sai ya yi kira ga kungiyar ta G20 da ta tunkari wadannan matsaloli yadda ya kamata, ta lalubo matakan magancesu, da taimakawa wajen hado kan dukkanin sassa masu ruwa da tsaki, zuwa turbar goyon bayan juna da hadin gwiwa.
Kazalika, ya yi kira da a kara azamar daga muryoyin kasashe masu tasowa, da gina tsarin adalci, da budaddiyar odar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen duniya.
A cewarsa, kasar Sin ta fitar da tsarin gudanar da matakai, wadanda za su tabbatar da an aiwatar da manufofin G20 na bunkasa masana’antu a nahiyar Afirka da sauran kasashe masu karancin ci gaba. Yana mai jaddada aniyar Sin ta ingiza salon samar da ci gaban bai daya na dukkanin kasashen duniya.
Bugu da kari, Li ya ce Sin na goyon bayan rage basukan da ake bin kasashe masu tasowa, ta kuma shiga wani shiri tare da Afirka ta kudu, na tallafawa bunkasa masana’antu a Afirka. Kuma Sin din za ta kafa cibiyar kasa da kasa ta samar da ci gaba. (Saminu Alhassan)














