Firaministan kasar Sin Li Qiang zai halarci bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin CIIE karo na 7, da kuma tarurruka masu nasaba, kana zai gabatar da jawabi.
Kakakin ma’aikatar kasuwancin kasar Sin He Yadong ya bayyana hakan yau Lahadi, inda ya ce, za a gudanar da bikin na CIIE karo na 7 daga ranar 5 zuwa ta 10 ga watan Nuwamba a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin. (Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp