Firaministan kasar Sin Li Qiang zai halarci taron shugabannin kasashen kungiyar BRICS na 17 da za a yi daga ranar 5 zuwa 8 ga wata, a birnin Rio de Janeiro na Brazil.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ce ta sanar da hakan a yau, inda ta kara da cewa, bisa gayyatarsa da firaministan Masar Mostafa Madbouly ya yi, Li Qiang zai kuma yi ziyarar aiki a kasar Masar daga ranar 9 zuwa 10 ga wata.
- Xi Ya Bukaci Kungiyoyin Matasa Da Dalibai Su Zurfafa Gyare-Gyare Da Kirkire-Kirkire Don Samun Sabbin Nasarori
- Me Ya Sa JKS Mai Tsawon Tarihin Sama Da Shekaru 100 Ta Dore A Kan Mulki
Game da ziyarar, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce taron tsarin hadin gwiwa na BRICS, shi ne na farko da aka gudanar, tun bayan shigar sabuwar memba wato kasar Indonesia, da sauran abokan huldar kungiyar 10.
Ta ce, tarin kasashe masu saurin samun ci gaban tattalin arziki da masu tasowa, da ma hukumomin kasa da kasa da na shiyyoyi, sun samu gayyata. Sin na fatan yin aiki kafada da kafada da dukkanin bangarori, wajen karfafa hadin gwiwar BRICS bisa matsayin koli, da sanya gudummawar BRICS ta zama mai ingiza cudanyar mabambantan sassa, da mara baya ga ci gaban bai daya, da kyautata tsarin jagorancin duniya, da ci gaba mai inganci na “Babban rukunin hadin gwiwar BRICS”.
Mao Ning ya kuma bayyana cewa, a shekarun baya-bayan nan, dangantakar Sin da kasar Masar ta kara kyautata, kana sassan biyu sun zurfafa amincewa juna ta fuskar siyasa, da hadin gwiwa na zahiri a fannoni daban daban, wadanda suka haifar da manyan nasarori, sun kuma kusanto, da karfafa hadin kai a matakai daban daban.
Ta ce, yayin ziyarar, firaministan kasar Sin Li Qiang, zai zurfafa musayar ra’ayoyi tare da jagororin kasar Masar, game da ciyar da alakar sassan biyu gaba, da zurfafa hadin gwiwa mai samar da gajiya, da batutuwan dake jan hankulan sassan biyu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp