A yayin wata zantawa da ya yi da ‘yar jaridar babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG kwanan nan, firaministan kasar Singapore, Lee Hsien Loong, ya bayyana cewa, shawarar “ziri daya da hanya daya”, hanya ce da kasar Sin ke bi wajen bayar da gudummawa ga ci gaban shiyyar ta.
Singapore, ita ce kasa ta farko a cikin kasashe membobin kungiyar ASEAN, da ta bayyana goyon-bayan ta ga shawarar “ziri daya da hanya daya” a fili. Game da wannan batu, Lee ya ce, shawarar na taimakawa kasar Sin shiga cikin tsarin hadin-gwiwa da mu’amalar kasashen shiyyar ta, da cimma moriyar juna, abun da ya sa take samun maraba daga dukkanin fadin shiyyar. Kaza lika, ci gaban shiyyar na bukatar muhimman ababen more rayuwar al’umma, wadanda ke bukatar zuba jari. Kasar Sin tana da kwarewa wajen inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma, da iya samar da jari, har ma za ta iya karfafa alakar tattalin arziki da kasuwanci a tsakaninta da kasashen shiyyar.
Ya kara da cewa, shawarar “ziri daya da hanya daya” na taimakawa ainun wajen cimma wadannan burika. (Murtala Zhang)