Tsohon shugaban majalisar dattawan Nijeriya kuma Wazirin masarautar Ilorin, Dr. Abubakar Bukola Saraki, ya bayyana cewa; bayan ficewar gwamnan jihar Delta daga jam’iyyar PDP zuwa APC, ina ta samun kiran waya daga shugabanni da ƴan jam’iyya matasa da maza da mata, waɗanda suka tsaya tsayin daka wajen ganin an samu ci gaban dimokuraɗiyya.
Yawancin masu kiran waya suna son su ji matsayata a kan fitar gwamnan jihar Delta da ƴan tawagarsa.
- Wasanni Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Ci Gaban Matasa — Gidauniyar Bukola Saraki
- Kotu Ta Wanke Tsohon Dogarin Bukola Saraki Kan Zargin Biliyan ₦3.5b
Matsaya ta akan wannan magana shi ne, waɗanda ke son barin PDP su fita tun yanzu, su bar sauran da ke son ci gaba, mu mayar da hankali wajen sake gina jam’iyyar.
Yana da muhimmanci duk ɗan Nigeriya ya sani cewa dole ne a tashi tsaye wajen tabbatar da dimokuraɗiyya. Domin tabbatar da hakan, dole ne a samu jam’iyyu masu ƙarfi domin tursasa gwamnati ta yi abin da ya kamata.
Maganar zama jam’iyya ɗaya a ƙasar nan ba abu bane wanda zai zama alheri kasancewar ƙasa ce mai addinai daban-daban da ƙabilu daban-daban da yare daban-daban. Ai abin tsoro ne ma a ce a zauna babu wasu jam’iyyu sai jam’iyya ɗaya, hakan zai nuna cewa mutane ba su da zaɓi, duk abin da aka ga dama shi za a yi musu.
Saboda haka akwai buƙatar duk wani ɗan ƙasa ya tsaya tsayin daka wajen ganin an samu jam’iyyar adawa mai ƙarfi, wadda za ta karɓi mulki daga hannun jam’iyya mai mulki.
Saƙona ga ƴan jam’iyya shi ne duk wanda yake son ya tafi ga hanya nan, wanda yake son gyara kuma ya zauna a gyara domin mu samu mutane masu amana, waɗanda za mu dinga rufe ƙofa da su kuma ba za su fitar da maganar a waje ba.
Halin da ake ciki yanzu ya bayyana irin matsayar da mutane irina suke kai tun farko na yin shiru domin ganin yadda abubuwa suke tafiya. Tabbas na yadda cewa babu gaskiya a wajen wasu shugabannin daga jam’iyya mai mulki domin yanzu baka san da wa zaka amince kayi maganar sirri ba.
Ya zama dole ƴan jam’iyyar PDP su daina zargin jam’iyya mai mulki da kawo rikici a PDP, domin hakan nuna gazawa ne domin kowa yana yin yadda zai yi ne domin ya samu nasara a zaɓe. Saboda haka ya zama dole a san abin yi, a yi aiki tuƙuru wajen kawo gyara a jam’iyyar PDP.
Tabbas akwai takaici a ce mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen da ya gabata ya fice daga jam’iyya ya koma jam’iyya mai mulki, babu wanda zai gaya maka wani dalilii mai ƙarfi na yin hakan. Kawai hakan yana nuna rashin manufa ne da yadda muka lalace a siyasance.
Tun farko daman shi ne dalilin da yasa nake yawan cewa mu ƙarfafa tsarin mulki da hukumomi a kan ƙarfafa wani mutum guda ɗaya. Duk da fitar gwamnan jihar Delta, har yanzu muna da damar cin zaɓe a ƙasar nan.
Ƴan jam’iyyar mu ya kamata su nutsu, su samu ƙwarin gwiwa domin samun nasara. Mu kalli wannan halin da muke ciki a matsayin wani darasi da zai sa mu sake gina jam’iyyarmu. Akwai nasara a nan gaba
Ina da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba shugabancin jam’iyya a matakai daban-daban zai sake zama domin tattauna halin da ake ciki da kawo mafita. Saboda haka babu tashin hankali a cikin abin da ke faruwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp