Fastan nan mai suna Rev. Azzaman David, shugaban majami’ar The King Worship Chapel da ke Kaduna, ya rasu a wani hatsarin mota a ranar Asabar yayin dawowarsa daga Makurdi, jihar Benue zuwa Kaduna.
Shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) na Jihohin Arewa 19 da FCT, Rev. John Joseph Hayab, ya tabbatar da mutuwar fastan, inda ya bayyana cewa al’ummar Kirista ta yi hasarar babban jarumi.
“Evangelist Azzaman ya kasance mai himmar wa’azi, mai kare addinin Kirista, kuma mai fafutukar kare hakkin masu ƙaramin ƙarfi. Rayuwarsa ta kasance cikin jarumtaka da ƙwarin gwuiwa ga gaskiya da adalci,” in ji Hayab.
CAN ta yi wa iyalansa, da ‘yan cocinsa, da duk wanda rayuwarsa ta shafa ta’aziyya, tare da addu’ar Allah ya ba su ƙarfin zuciya a wannan lokacin baƙin ciki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp