Hukumar IMF ta nuna damuwa kan fitar da kudade ta haramtacciyar hanya daga Nijeriya, inda ta ce hakan na kara dagula matsalar samun kudaden shiga na kasar.
Manajiyar Darakta ta hukumar, Mis Kristalina Georgieba, wadda ta bayyana hakan a taron shekara na 2025 na IMF da Bankin Duniya a birnin Washington DC, ta yi alkawarin mayar da hankali wajen bin diddigin irin wadannan kudade domin rufe gibi a harkokin kudi na gwamnati.
- Kotu Ta Ɗaure Mai Horas Da ‘Yan Wasa Shekaru 8 Sakamakon Zargin Luwaɗi Da Ƙaramin Yaro A Kano
- Batun Yin Afuwa Ga ‘Yan Yankin Ogoni Huɗu
Ta ce: “Muna ganin cewa, ga kasashe irin su Nijeriya, mayar da hankalin IMF wajen bin diddigin fitar da kudade ta haramtacciyar hanya zai iya zama tsari na magance gibi a harkokin kudi da ya dade yana hana samun kudaden shiga da kuma ci gaba mai dorewa.”
Georgieba ta kuma gargadi duniya kan barazanar da fitar da kudade ta haramtacciyar hanya (IFFs) ke yi, inda ta ce wannan matsala ta zama babbar abin da ke lalata tattalin arziki da tsarin kudi na kasashe a fadin duniya.
A cewarta, fitar da kudade ta haramtacciyar hanya wacce ta hada da satar kudaden gwamnati, kudaden da suka fito daga ayyukan laifi, da mu’amalolin dijital da ba a iya bibiyarsu na ci gaba da lalata tsarin mulki, rage kudaden gwamnati, da durkusar da kokarin ci gaba, musamman a kasashe masu tasowa.
A cikin wani jawabin manufofi na baya-bayan nan, jami’an IMF sun bayyana cewa IFFs yanzu suna zuwa ta fannoni da dama. Wannan ya hada da karkatar da kudaden haraji kai tsaye zuwa aljihun wasu mutane da kuma karkatar da kudaden masu zaman kansu zuwa haramtattun harkoki da ke barazana ga jin dadin kasa.
Sun kara da cewa tattalin arzikin dijital ya kara tsananta wannan matsala, inda kudaden dijital kamar Bitcoin ke ba da damar yin mu’amalolin kudi ba tare da a san masu aikata su ba.
Shugabar IMF ta ce: “Za ka iya samun kudi, kudin da aka sace kai tsaye daga al’ummar masu biyan haraji. Haka kuma akwai kudaden masu zaman kansu da ake karkatawa zuwa ayyukan laifi da ke lalata jin dadin ‘yan kasa.”
“Yanzu da kudaden dijital, ana iya tallafa wa ayyukan laifi ba tare da a gano su ba. Wannan babbar matsala ce, kuma dole ne mu dauke ta da muhimmanci.”
Dabarar IMF Wajen Yakar Kudaden Haram:
A martaninta, IMF ta bayyana cewa ta karfafa tsarinta na yaki da safarar kudade da kuma hana tallafa wa ta’addanci (AML/CFT) bayan cikakkiyar bita da aka gudanar a shekarar 2023.