Sanata Solomon Adeola mai wakiltar (mazabar majalisar dattawa ko kuma Ogun ta Yamma karkashin jam’iyyar APC) ya nuna jin dadinsa akan irin nasarar da aka samu lokacin rajisata masu neman rubuta jarabawar shiga manyan makarantu wato JAMB inda ya bada damar yin hakan ga dalibai wadanda suka fito daga mazabarsa.
A wata sanarwar ta mai bashi shawara kan harkokin watsa labari Chief Kayode Udunaro ya rabawa manema labarai a Abuja.Sanata ya na bayanin ne bayan rahoton kwamitin daya nada/ kafa domin bunkasa ilimi, wanda aka mika ma sa,ya jinjinawa shi kwamitin wanda ya bada damar yi wa dalibai ‘yan asalin mazabar ta sa 4,200 daga cikin 5,000 wadanda dama niyyar yin hakan ke nan.
- An Kashe Askarawa 6 da ‘Yan Sa-kai 4 A Zamfara
- Yadda Tinubu Ya Shirya Wa Kansa Mafitar Siyasa Kafin Zaben 2027
Ya nuna jin dadinsa inda yace daga karshe wadanda suka amfana da tallafin nasa suna iya kasancewa masu nasarar samun guraben karatu bayan rubuta jarabawar
Rahoton kwamitin da aka kai zuwa ofishin Sanatan dalibai 5,000 wadanda tun farko sune aka yi niyyar yi wa rajista hakan ba zai samu ba hakan kuwa ya biyo bayan rufe damar yin rajisatar da aka yi ranar 24 ga watan Fabrairu 2025, da kuma yadda aka rika samun matsalar rashin bada damar rajisata ta kafar sadarwa ta zamani.
Mista Scholar Ola Agbetokun, wanda jagora ne na tsarin ya bayyana an zabo wadanda suka yi rajisatar ne daga Kananan Hukumomi biyar na Ogun ta yamma wadanda suka hada da Ado Odo Ota, Yewa ta Kudu, Yewa ta Arewa, Ipokia, da kuma Imeko Afon.
Ya kara bayanin cewa an dauki matakin ne inda har abin ya shafi daliban da suke mazabun majalisar Dattawa biyu na Jihar Osun.
Ya nuna jin dadinsa inda ya furta ce wa“Wani abin farinciki ne gare ni dana samu yawan daliban da suka samu damar yin rajista daga mazaba ta da kuma saiuran mazabun na majalisar Dattawa, wadanda su basu samu damar rubuta jarabawar da zata basu damar zuwa manyan makarantu ba a fadin tarayyar Nijeriya.
“Ilimi shi ne wani babban abinda ya kamata kowane dan/ ‘yar kasa su kasance sun samu damar yin haka ta samun sa, don haka lamarain kudi bai dace ace ya hana su damar samun hakan ba musamman ma ga matasa wadanda sune manyan gobe kamar yadda Sanatan ya bayyana”.
Daga karshe ya yi karin bayani ne na shit sarin bada fom domin cikawa saboda rubuta JAMB wata dama ce ita ma tayi kama ko daya take da damar bada guraben karatu zuwa manyan makarantu, na dalibai 500 za a cimma burin yin haka cikin makonni masu zuwa na gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp