• English
  • Business News
Sunday, July 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Tinubu Ya Shirya Wa Kansa Mafitar Siyasa Kafin Zaben 2027

by Idris Aliyu Daudawa and Sulaiman
3 months ago
in Manyan Labarai, Rahotonni
0
Tinubu
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Yayin da ‘yan siyasa suke ta jiran a fara buga Tambarin siyasa, a cikin shirin da ake yi na babban zabe na shekara 2027,da akwai alamun da suke nuna cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da yawancin mambobin majalisun kasa wadanda suke kan karagar su yanzu,a karkashin tutar jam’iyyar APC ana ganin za a basu damar takara ba tare da yin zaben fidda gwani ba.

Wata majiya daga jam’iyyar mai mulki ta bayyanawa jaridar LEADERSHIP cewa shi matakin wani babban lamari ne ga su masu fada aji na jam’iyyar, abinda suke yi wa kallon wata dama ce musamman ma yadda shi Shugaban kasa yake son a yi hakan ta tafiyar da hakan a fadin tarayyar Nijeriya zai ba jam’iyyar ko bada wata dama ce da suke ganin ba zata iya haduwa da wata matsala ba.

  • Matasa 4 Sun Yi Garkuwa Da Yaro, Sun Kashe Shi A Bauchi
  • Hikimar Gwamnatin Jihar Jigawa Na Kaddamar Da Shirin Gina Rijiyoyin Burtsatsan Noman Rani

Kamar yadda daya daga cikin majiyar tamu ta bayyana akwai maganar bada damar tsayawa takara ta kai tsaye,ba tare da,yin zaben fidda gwani ba,an kuma bullo da, ita shawarar ne domin a hana yiyuwar daukar matakai/mataki na zuwa kotu wanda wadanda basu samu damar samun tikitin ba,suna iya yin amfani da hakan abinda ake yiwa kallon, hakan ne zai iya kawowa jam’iyyar wani cikas ko“goga mata kashin Kajin da watakila ba zai iya wankuwa bako da wane irin ruwa ne,”a shirin da ake yi na zaben 2027.

Hari la yau majiyar ta ce shawarar tana daga cikin dalilan da suka sa wasu ‘yanmajalisar Adawa, a majalisun biyu suka koma jam’iyyar APC.

Hari la yau da akwai majiyar data ce akwai abinda aka lura da shi wato yin biyayya ga jam’iyya, da kasancewa jam’iyya tsintsiya daya madaurinki daya,wanda idan ba sa’a aka yi ba idan har aka yi zaben fidda gwanin hakan na iya samar da matsalar cikin gida ta jam’iyya lamarin da zai iya samar da karin rarrabuwar kai.

Labarai Masu Nasaba

Ku Manta Da 2027, Tinubu Zai Ci Gaba Da Mulki Har 2031 — Fadar Shugaban Ƙasa Ga ADC

Kwankwaso Ba Zai Sake Yi Mana Takarar Shugabancin Ƙasa Ba A Zaɓen 2027 Ba – NNPP

Ita maganar bada damar tsayawa takara ba tare da zaben fidda gwani ba an dauki matakin ne saboda yadda aka ga ‘yan adawa ko jam’iyyun adawa suke kokarin tayar da babbar kura mai hayaki,wa ita jam’iyyar mai rike da kambun mulki a 2027 domin “Ba a san maci Tuwo ba sai Miya ta kare”.

Ana dai ganin tarurrukan da aka yi na mambobin APC,wadanda suke ganin ba,a kyauta masu ba da kuma Shugabannin adawa suna yin wani shiri wanda zai iya sa wasu daga cikinsu su yi jerin Tururuwa na komawa jam’iyyar SDP,kamar dai yadda tsohon Gwamnan Jihar Kaduna,Malam Nasiru El Rufa’i ya fara kasancewa na farko wanda ake ganin akwai wadanda za su iya goyo masa baya.

Idan dai ba a manta ba mako biyu da ya wuce kwamitin zartarwar jami’iyyar ya nuna amincewa da ayyukan da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi,hakan yana nuna ko dai su amince da bashi tikitin takara k kuma akashin hakan.

Akwai majiya mai tushe da ta bayyana a cikin taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar da aka yi a Abuja ya nuna cewa kamar yadda abin yake an tattauna ne kan yadda tsarin Shugabancin jam’iyyar yake tun daga sama zuwa kasa,ko kuma daga na kasa, Jiha, Karamar Hukuma har zuwa na mazabar Kansila (Ward) an tattauna komai kan hakan.

Akwai majiyar da bata son a ambacin sunanta, da yi bayanin akwai wasu daga cikin Gwamnonin da basu amince da lamarin ba gaba daya ba,su ma da akwai wani tsarin da ake yi wanda zai basu damar su zabi wadanda suke son tsayawa takarar majalisar Jiha a Jihohinsu.

Idan har shi tsarin da aka yi an samu yin amfani da shi kwatin zartarwar jam’iyyar na kasa karkashin jagorancin Dakta Umar Abdullahi Ganduje da takwarorinsu na Jihohi za a barsu su ci gaba da tafiyar da jam’iyyar,saboda su taimakawa shirin da ake yi na kasancewar Bola Ahmed Tinubu shi ne dan takarar jam’iyyar.

Dankararar jam’iayyr daya tilo,suma ‘yan majalisun Dattawa da Wakilai wadanda suka ba jam’iayyar goyon baya tun daga lokacin da,Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fara mulki.

“Shugabannin jam’iyyar sun san kura- kuren da aka yi a baya wanda matsala ce ta cikin gida wadda ta so sa wa jam’iyyar wani babban Tarnaki abinda daga karshe ya sa lakar jam’iyya ta kasance tamkar “Kazar da Kwai ya fashe ma ta a Ciki”. Wannan lokacin, ana bukatar ne kada a samu wata matsalar da zata iya kawo koma-baya. Hanya mafi dacewa ta yin hakan ita ce a ci gaba da tafiya irin yadda TSARIN Shugabancin jam’iyyar APC ya tsara ayi, domin a kaucewa aukuwar lamarin da zai sa ayi ta yin kumfar Baki saboda zaben fidda gwani.

“Idan za a tuna a zaben shekarar 2019, a babban zaben a Jihar Zamfara, mun rasa Jihar Zamfarar ne “inda jam’iyyar PDP ta samu dame a kala”,saboda rikicin cikin gida wanda ya fara ne sanadiyar zaben fidda gwani wanda aka ci gaba har zuwa 2023.

“Hakanan ma jam’iyyar APC, bata da ‘yan takara a Jihar Ribas saboda zaben fidda gwanin da mambobin jam’iyyar suka yi sau biyu kuma mabambanci.Hakanan ma akwai matsala wadda zaben Shugabannin jam’iyyar ya kusan gamawa da Jihar Imo. Idan ba lamarin kotu ba mun kusa rasa kujerar mu jam’iyyar PDP ta samu.”

Shugaban kasa ya samu rahoton sirri wanda ya nuna wadansu ‘yan jam’iyyar ba a kyautata masu ba, suna shirin barin jam’iyyar su koma wasu jam’iyyun adawa.

“Salon farko na su shi ne su samar da matsala cikin jam’iyyar APC idan an yi sabon zaben Shugabannin jam’iyyar.Domin maganin hakan, hanya mafita ita ce kada ayi zaben Shugabannin jam’iyyar,da kuma zaben kasa na jam’iyyar kafin babban zaben 2027.

“Hankalin sa kwance yake wajen tabbatar da babu wata matsala cikin jam’iyya,da kuma hana yiyuwar rigingimun bayan zabe wadanda suna iya kawo koma- baya. Ci gaba da wadannan Shugabannin ita ce mafita kuma zai taimaka wajen samun kwanciyar hankali kamar yadda majiyar ta ce”.

An samu labarin cewa jam’iyyar tana son ta amince da wata doka tunda har yanzu ba a bada sanarwa game da zaben kasa wanda za a ci gaba da tafiya da Shugabannin da ake da su a ci gaba da tafiya da su,tun daga na kasa har zuwa ta karshe ta matakin mazabar Kansila wato ward ke nan.

Matakin zai kara karfin Tinubu kan yadda taswirar jam’iyyar ta ke da kuma zabubbukan fidda gwani.

“Jam’iyyar ta shirya yadda zata zabi Shugabannin ta wanda a ranar ce, wani zai bada shawarar cewa a ci gaba da tafiya da Shugabnnin da ake fara tafiyar da su,tun daga na kasa har zuwa Ward har sai bayan babban zabe na shekarar 2027 kamar yadda bayanin ya nuna”.

Wadanda ake damawa da su a jam’iyya sun ce matakin shi ne abinda aka fi amincewa da shi, watao kwamitin zartarwar kasa na jam’iyyar ya amince da yadda Ganduje ya tafiyar da aikinsa tare da kwamitin gudanarwar sa.Matakin ya amince ne da yadda suka iya tafiyar da jam’iyyar duk kuwa da ta fuskanci matsaloli ma su yawa.Duk da hantarar da suka rika fama da ita sai da suka yi duk yadda suka iya suka samu aka amince da shi ne dantakarar ta na Shugaban kasa a shekarar 2027 ba tare da bata wani lokaci ba.

Hakanan ma ‘yan majalisun Dattawa dana Wakilai na jam’iyyar suma za su amfana da tsarin jam’iyyar su sake tsayawa ba tare da wata hamayya ba.

“Akwai maganar amincewa a jam’iyya kan lamarin amincewa da sa ita jam’iyyar ta sa kanta yin wani abinda zai iya kawo masu ko mata matsala. Yawancin ‘yan jam’iyyar da suke majalisun Dattawa da na Wakilai wadanda suka nunawa jam’iyyar ladabi da shi Shugaban kasa,ba sai sun tsaya sun fuskanci zabubbukan tantance gwani ba.Maimakon haka ma dama ce kawai za a basu su, su sake tsayawa takara ba tare da wata matsala ba sais u sake komawa kujerar tasu,”cewar wani babban kusa a jam’iyyar da baya son a ambaci sunansa.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [15]

Next Post

Gwamnatin Kano Ga Ma’aikata: Duk Mai Bukatar Aikinsa Dole Ya Gabatar Da Kansa A Wajen Tantancewa

Related

Ku Manta Da 2027, Tinubu Zai Ci Gaba Da Mulki Har 2031 — Fadar Shugaban Ƙasa Ga ADC
Manyan Labarai

Ku Manta Da 2027, Tinubu Zai Ci Gaba Da Mulki Har 2031 — Fadar Shugaban Ƙasa Ga ADC

6 hours ago
Kwankwaso Ba Zai Sake Yi Mana Takarar Shugabancin Ƙasa Ba A Zaɓen 2027 Ba – NNPP
Manyan Labarai

Kwankwaso Ba Zai Sake Yi Mana Takarar Shugabancin Ƙasa Ba A Zaɓen 2027 Ba – NNPP

13 hours ago
Gwamna Ademola Adeleke Ya Ƙaryata Jita-Jitar Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC
Manyan Labarai

Gwamna Ademola Adeleke Ya Ƙaryata Jita-Jitar Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC

17 hours ago
‘Yansanda Sun Kama Barayi 15, Sun Kwato Motocin Sata 20 A Kano
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Kama ’Yan Bindiga 17 Tare Da Kashe 3 A Abuja

1 day ago
Kotu Ta Umarci Majalisar Dattijan Nijeriya Da Ta Gaggauta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Natasha
Manyan Labarai

Kotu Ta Umarci Majalisar Dattijan Nijeriya Da Ta Gaggauta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Natasha

2 days ago
Zanga-zangar ‘Yan Gudun Hijira Na Yelewata ‘Yar Manuniya Ce Ga Daukar Matakan Da Suka Dace
Manyan Labarai

Zanga-zangar ‘Yan Gudun Hijira Na Yelewata ‘Yar Manuniya Ce Ga Daukar Matakan Da Suka Dace

2 days ago
Next Post
Mauludi: Gwamnatin Kano Ta Sake Ɗage Ranar Komawa Makarantu

Gwamnatin Kano Ga Ma’aikata: Duk Mai Bukatar Aikinsa Dole Ya Gabatar Da Kansa A Wajen Tantancewa

LABARAI MASU NASABA

Wang Yi: Amfani Da Karfin Soji Ba Bisa Ka’ida Ba Na Ingiza Karuwar Tashin Hankali

Wang Yi: Amfani Da Karfin Soji Ba Bisa Ka’ida Ba Na Ingiza Karuwar Tashin Hankali

July 5, 2025
Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Na Cike Da Hangen Nesa Da Burikan Samar Da Ci Gaba In Ji Firaministan Kasar Senegal

Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Na Cike Da Hangen Nesa Da Burikan Samar Da Ci Gaba In Ji Firaministan Kasar Senegal

July 5, 2025
‘Yan Adawa Sun Dunkule A ADC Don Tunkarar Tinubu A 2027

‘Yan Adawa Sun Dunkule A ADC Don Tunkarar Tinubu A 2027

July 5, 2025
Wakilin Sin Ya Yi Jawabi Game Da Raya Hidimomi Ga Nakasassu Ta Hanyar Fasahar AI A Madadin Wakilan Kasashe Fiye Da 70

Wakilin Sin Ya Yi Jawabi Game Da Raya Hidimomi Ga Nakasassu Ta Hanyar Fasahar AI A Madadin Wakilan Kasashe Fiye Da 70

July 5, 2025
Ku Manta Da 2027, Tinubu Zai Ci Gaba Da Mulki Har 2031 — Fadar Shugaban Ƙasa Ga ADC

Ku Manta Da 2027, Tinubu Zai Ci Gaba Da Mulki Har 2031 — Fadar Shugaban Ƙasa Ga ADC

July 5, 2025
Zan Dade Ban Manta Da Mahaifinmu Ba -Abba Sadau

Zan Dade Ban Manta Da Mahaifinmu Ba -Abba Sadau

July 5, 2025
Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN Ta Nuna Goyon Baya Ga Fadadar Kungiyar BRICS A Matsayin Hanyar Bunkasa Hadin Gwiwa

Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN Ta Nuna Goyon Baya Ga Fadadar Kungiyar BRICS A Matsayin Hanyar Bunkasa Hadin Gwiwa

July 5, 2025
Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi

Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi

July 5, 2025
Wang Yi Da Takwaransa Na Ghana Sun Aikewa Juna Sakon Murnar Cika Shekaru 65 Da Kulla Dangantakar Diplomasiyya A Tsakanin Kasashensu

Wang Yi Da Takwaransa Na Ghana Sun Aikewa Juna Sakon Murnar Cika Shekaru 65 Da Kulla Dangantakar Diplomasiyya A Tsakanin Kasashensu

July 5, 2025
Sin Da Faransa Sun Amince Da Ingiza Cudanyar Mabanbantan Sassa Tare Da Samar Da Karin Tabbaci Ga Duniya

Sin Da Faransa Sun Amince Da Ingiza Cudanyar Mabanbantan Sassa Tare Da Samar Da Karin Tabbaci Ga Duniya

July 5, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.