Wani rahoton bincike da aka fitar a yau Jumma’a, ya nuna cewa jarin da kamfanonin kasar Sin ke zubawa a kasashen waje ya karu sannu a hankali a shekarar 2024, inda fiye da kaso 80 cikin dari na kamfanonin ke ci gaba da gudanar da harkokin jarin da suka zuba ko kuma fadada shi a kasashen waje.
Fiye da kaso 90 cikin dari na kamfanonin da aka gudanar da binciken a kansu, sun nuna kwarin gwiwa da yakini a kan tarin albarkar da ke cikin zuba jari a kasashen waje, kamar yadda binciken wanda hukumar bunkasa harkokin cinikayyar kasashen waje ta kasar Sin ko CCPIT a takaice ta gudanar ya bayyana.
Binciken ya kuma gano cewa kamfanonin na Sin sun fi nuna sha’awar zuba jari a kasashe da yankunan da ke cikin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, kamar yadda mai magana da yawun CCPTI Sun Xiao ya ayyana a wani taron manema labarai a yau. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)