Hukumar kula da fansho ta kasa ta bayyana cewa a shekarar da ta shude ta biya sama da naira miliyan 326 ga ma’aikatan da suka yi ritaya.
Bayanin haka na kunshe a cikin wani rahoton da hukumar ta fitar na shekara-shekara a Abuja.
- Yunkurin Amurka Kan Sana’ar Kera Sassan Na’urorin Laturoni Ba Zai Yi Nasara Ba
- Gwamna Wike Ya Karyata Cire Tutocin PDP Daga Gidan Gwamnatin Jihar Ribas
Rahoton ya bayyana cewa a shekarar da ta gabata an biya kimanin naira miliyan 442 a matsayin kudaden fansho na ma’aikatan gwamnatin tarayya da jihohi da na kananan hukumomi.
Hukumar ta kara da cewa daga watan farko zuwa ranar 31 ga Disambar shekarar da ta shude, kudaden fanshon da aka karba daga bangarori masu zaman kansu sun kai naira miliyan 327 a shekara ta 2020, inda suka karu zuwa naira miliyan 366 a shekarar da ta gabata.
Hukumar ta gudanar da shirin tantance ‘yan fansho a kananan hukumomin Funtua, Bakori, Danja, Dandume, Faskari da Sabuwa wanda ya gudana ba tare da wata matsala ba.
Da yake gabatar da jawabi, sakataren hukumar, Alhaji Mustapha Abdullahi Bujawa ya yaba da halin dattakun da ‘yan fanshon suka nuna a lokacin gudanar da shirin.
Alhaji Mustapha ya yi kira ga ‘yan fanshon da su ba da goyon baya da hadin kai ga jami’an da ke gudanar da shirin, domin samun nasarar ga wannan aiki.