• Leadership Hausa
Tuesday, May 30, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Wike Ya Karyata Cire Tutocin PDP Daga Gidan Gwamnatin Jihar Ribas

by Muhammad
10 months ago
in Siyasa
0
Gwamna Wike Ya Karyata Cire Tutocin PDP Daga Gidan Gwamnatin Jihar Ribas
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike, ya karyata rahotannin da ake yadawa a shafukan sada zumunta cewa ya bayar da umarnin cire tutocin jam’iyyar PDP daga gidan gwamnati da ke Fatakwal.

Wannan na zuwa a daidai lokacin da sakataren yada labaran jam’iyyar adawa ta APC a jihar, Senibo Chris Finebone, ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyyar zuwa PDP.

  • Zaben Fidda Gwanin PDP: Wike Ya Gurfanar Da Atiku, Tambuwal Da INEC A Gaban Kotu
  • Me Ya Sa Ake Rubibin Wike A Siyasar Nijeriya?

A safiyar ranar Juma’a an wayi bari ko’ina a kafafen sada zumunta da hoton Finebone tare da gwamnan jihar Ribas, Wike, dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, Siminalaye Fubara, da kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC, Cif Davies Ibiamu Ikanya, a wata ziyara da suka kai gidan gwamnan a Fatakwal a daren Alhamis.

Wike, wanda ya yi magana a daren Alhamis a Fatakwal, babban birnin jihar, yayin da yake karbar Finebone da Ikanya, ya ce: “Kuna iya tunani kan irin labaran karya da mutane ke yadawa. Ba na bata lokacina akan irin wannan karyar.”

Da yake mayar da martani kan kalaman tsohon kakakin jam’iyyar APC, gwamnan ya yi alkawarin bayar da kwangilar gina titin Opobo Ring kafin ya bar mulki a shekarar 2023.

Labarai Masu Nasaba

Kwana 2 Kafin Rantsuwa: Kotun Koli Ta Yi Watsi Da Karar PDP Kan Takarar Tinubu Da Shettima

Jam’iyyar Labour Ta Yi Fatali Da Hukuncin Da Kotu Ta Yanke Kan Zababben Gwamnan Abia

Ya ce: “Zan bayar da kwangilar titin Opobo Ring Road kuma na kuma tabbatar da cewa an samar da kudin da zan biya kafin in bar ofis a watan Mayun 2023.

“Allah ne yasa danka ya zama dan takarar gwamna a jam’iyyarmu. Haka Allah zai sa shi ya ci nasara. Ban shirya ba amma Allah ne ya yi. Jama’ar Opobo su rika godewa Allah da jinkansa”.

Da yake tabbatar da komawarsa jam’iyyar PDP mai mulki, Finebone ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa; “Sim Fubara yayana ne.”

ShareTweetSendShare
Previous Post

Labarin Asadulmuluuk (36)

Next Post

Shin Kana Tuna Wadannan Idan Za Ka Aikata Zunubi?

Related

Kwana 2 Kafin Rantsuwa: Kotun Koli Ta Yi Watsi Da Karar PDP Kan Takarar Tinubu Da Shettima
Siyasa

Kwana 2 Kafin Rantsuwa: Kotun Koli Ta Yi Watsi Da Karar PDP Kan Takarar Tinubu Da Shettima

3 days ago
Jam’iyyar Labour Ta Yi Fatali Da Hukuncin Da Kotu Ta Yanke Kan Zababben Gwamnan Abia
Siyasa

Jam’iyyar Labour Ta Yi Fatali Da Hukuncin Da Kotu Ta Yanke Kan Zababben Gwamnan Abia

1 week ago
Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Soke Nasarar Zababben Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti
Manyan Labarai

Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Soke Nasarar Zababben Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti

2 weeks ago
Tinubu Da Kwankwaso Sun Gana A Faransa
Manyan Labarai

Tinubu Da Kwankwaso Sun Gana A Faransa

2 weeks ago
Zargin Dakatar Da Makarfi A PDP Tatsuniya Ce –Shugaba
Labarai

Zargin Dakatar Da Makarfi A PDP Tatsuniya Ce –Shugaba

2 weeks ago
APC Ce Za Ta Yi Nasarar Samar Da Shugabanci A Majalisa – Hon. Wase
Siyasa

APC Ce Za Ta Yi Nasarar Samar Da Shugabanci A Majalisa – Hon. Wase

2 weeks ago
Next Post
Shin Kana Tuna Wadannan Idan Za Ka Aikata Zunubi?

Shin Kana Tuna Wadannan Idan Za Ka Aikata Zunubi?

LABARAI MASU NASABA

Da Dumi-dumi: Hukumar DSS Ta Yi Wa Ofishin EFCC Kawanya, Ta Hana Jami’an Shiga Ginin

Da Dumi-dumi: Hukumar DSS Ta Yi Wa Ofishin EFCC Kawanya, Ta Hana Jami’an Shiga Ginin

May 30, 2023
Yadda Amurka Ta Yi Kokarin Amfani Da Nukiliya Wajen Tarwatsa Wata

Yadda Amurka Ta Yi Kokarin Amfani Da Nukiliya Wajen Tarwatsa Wata

May 30, 2023
Gwamnatin Kano Za Ta Sake Bude Shari’ar Zargin Kisan Da Ake Yi Wa Alhassan Doguwa 

Gwamnatin Kano Za Ta Sake Bude Shari’ar Zargin Kisan Da Ake Yi Wa Alhassan Doguwa 

May 30, 2023
Sabon Gwamnan Kano Ya Kori Shugaban Hukumar Alhazai Na Jihar Da Wasu

Sabon Gwamnan Kano Ya Kori Shugaban Hukumar Alhazai Na Jihar Da Wasu

May 30, 2023
Kamfanin NNPCL Ya Goyi Bayan Cire Tallafin Man Fetur, Ya Yi Alkawarin Samar Da Wadataccen Mai

Kamfanin NNPCL Ya Goyi Bayan Cire Tallafin Man Fetur, Ya Yi Alkawarin Samar Da Wadataccen Mai

May 30, 2023
Kasar Sin Ta Tuntuba Tare Da Musayar Ra’ayi Da Dukkan Bangarori Game Da Warware Rikicin Ukraine A Siyasance

Kasar Sin Ta Tuntuba Tare Da Musayar Ra’ayi Da Dukkan Bangarori Game Da Warware Rikicin Ukraine A Siyasance

May 29, 2023
Sin Da Afirka Sun Fi Bukatar Kara Hadin Gwiwa Da Juna

Sin Da Afirka Sun Fi Bukatar Kara Hadin Gwiwa Da Juna

May 29, 2023
Tinubu Ya Taya Erdoğan Murnar Nasarar Cin Zaben Shugaban Kasar Turkiyya

Tinubu Ya Taya Erdoğan Murnar Nasarar Cin Zaben Shugaban Kasar Turkiyya

May 29, 2023
Sabon Gwamnan Sakkwato Ahmed Aliyu Ya Nemi Goyon Bayan ‘Yan Adawa A Jihar

Sabon Gwamnan Sakkwato Ahmed Aliyu Ya Nemi Goyon Bayan ‘Yan Adawa A Jihar

May 29, 2023
An Wallafa Littafi Kan Jawabin Shugaba Xi Jinping A Wajen Taron Kolin Kasar Sin Da Yankin Tsakiyar Asiya

An Wallafa Littafi Kan Jawabin Shugaba Xi Jinping A Wajen Taron Kolin Kasar Sin Da Yankin Tsakiyar Asiya

May 29, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.