• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

FRSC Ta Fara Binciken Hatsarin Motar Da Ya Yi Ajalin ’Yan Wasan Kano 22

by Sadiq
5 months ago
Kano

Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), ta fara gudanar da bincike kan hatsarin motar da ya kashe mutum 22 daga tawagar ’yan wasan Jihar Kano yayin da suke dawowa daga Gasar Wasannin Ƙasa da aka kammala a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.

Shugaban FRSC na ƙasa, Shehu Mohammed, ya bayyana hakan lokacin da ya kai wa Gwamnatin Jihar Kano ziyarar jaje a ranar Litinin.

  • An Yi Balaguro Miliyan 657 A Tsakanin Yankunan Kasar Sin Lokacin Bikin Duanwu Na Bana
  • Hadin Gwiwa Hanya Ce Madaidaiciya Wajen Kiyaye Tsaron Shiyya

Ya samu wakilcin Kwamandan Shiyya ta ɗaya ta FRSC, Ahmad Umar, wanda ke matsayin Mataimakin Kwamanda Janar.

Hukumar ta ce wajen da hatsarin ya faru ya yi ƙaurin suna da yawan faruwar haɗuran mota.

“Muna da yaƙinin cewa haɗuran mota ba sa faruwa haka kawai ba akwai dalilai da ke haddasawa. Idan aka gane dalilan, za a iya hana afkuwarsu,” in ji jami’in.

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

Gwarzon Ma’aikacin Lafiya Na Shekarar 2025 Dakta Seidu Adebayo Bello

Ya ƙara da cewa FRSC ta fara bincike kan dalilan da ke jawo hatsarin, kuma za ta gabatar da sakamakon binciken ga hedikwatarta da kuma Gwamnatin Jihar Kano domin ɗaukar matakan da suka dace don hana irin faruwar irin wannan iftila’i a gaba.

Hukumar ta kuma sake jaddada ƙudirinta na wayar da kan al’umma kan amfani da hanya yadda ya dace da kiyaye lafiyar masu amfani da hanya.

A nasa ɓangaren, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Gwarzo, ya wakilta, ya gode wa FRSC bisa ziyarar.

Ya bayyana damuwarsa cewa wajen da hatsarin ya faru ya daɗe yana haddasa mummunan haɗura, inda ya bayyana cewa gwamnati za ta yi duk abin da ya kamata don hana faruwar hakan a nan gaba.

“Idan kun san wani waje da ke da hatsari a cikin gari ko wajen gari, ka da ku yi shiru. Ku sanar da gwamnati. Wannan aiki ne da za mu tashi gaba ɗaya domin shawo kansa,” in ji shi.

Ya bayyana mutuwar ‘yan wasan 22 a matsayin abin firgici da tashin hankali, yana mai cewa ziyarar da FRSC ta kai ya nuna alhini da tausayi ga al’ummar Kano da iyalan waɗanda lamarin ya shafa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu
Manyan Labarai

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Manyan Labarai

Gwarzon Ma’aikacin Lafiya Na Shekarar 2025 Dakta Seidu Adebayo Bello

October 25, 2025
Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria
Tattalin Arziki

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

October 25, 2025
Next Post
Bello Yabo Ya Je Wajen Wa’azi Da Bindiga A Sakkwato, Ya Ce Ya Shirya Kare Kansa

Bello Yabo Ya Je Wajen Wa'azi Da Bindiga A Sakkwato, Ya Ce Ya Shirya Kare Kansa

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

October 25, 2025
An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC

An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC

October 25, 2025
Zuwan Tsoffin ’Yan Wasan Barcelona Abuja Ya Nuna Ana Samun Zaman Lafiya A Nijeriya – Matawalle

Zuwan Tsoffin ’Yan Wasan Barcelona Abuja Ya Nuna Ana Samun Zaman Lafiya A Nijeriya – Matawalle

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Lafiya Na Shekarar 2025 Dakta Seidu Adebayo Bello

October 25, 2025
Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

October 25, 2025

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kaya Na Shekarar 2025, Kamfanin Nestlé Pure Life

October 25, 2025
Mata Ne Ginshikin Ci-Gaban Al’umma – Gimbiyar Dange

Mata Ne Ginshikin Ci-Gaban Al’umma – Gimbiyar Dange

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales

October 25, 2025
Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce

Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Hukumar Kare Ƴancin Masu Amfani Da Kaya (FCCPC): Tabbatar Da Adalci A Kasuwa

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.