Hukumar kiyaye hadurra ta kasa reshen jihar Yobe ta nuna damuwarta kan karuwar yawan hadurra a kan hanyoyin da ke jihar.
Ya ce sau da yawa gudun wuce kima da kuma karya dokokin hanya ke yawan kawo hatsari a wasu manyan tituna da ke jihar Yobe.
- Obasanjo Ya Roki Marayun Borno Su Yafe Wa ‘Yan Ta’addar Da Suka Kashe Iyayensu
- Rashin Tsaro Na Kawo Koma Baya Ga Tattalin Arzikin Nijeriya – Buhari
Hukumar ta bayyana hakan ne a wata takarda da ta raba wa manema labarai a Damaturu wadda mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar Mohammed Kalli ya sanar da hannu, a cikin takardar Ida ya raba wa manema labarai.
Haka kuma hukuma ta nemi jama’a su zama masu kiyaye hatsari, domin tsira da ransu da lafiyarsu musammamn lokacin da suke kana bin hawa, saboda haka ne ma hukmar ta FRSC ta kara kaimi wajen ganin direbobi na bin dokar tuki ta shekara ta 2007 da ta 2016 wadda hukumar ta kafa, domin samun tsira da rayuka da kuma dukiyoyi.