Wasu fusatattun mutane da safiyar Lahadi sun kai hari kan wata ‘yar jarida ta gidan talabijin na Nijeriya (NTA), Mrs Pauline Kuje Vana, a lokacin da take bayar da labarin kan yadda gobarar ta tashi a babbar kasuwar Monday Market da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, lamarin ya faru a kasuwar litinin da ke Maiduguri da misalin karfe 1 na safiyar Lahadi inda ta kai har karfe 8:30 na safe duk da kokarin da jami’an kwana-kwana suka yi na ganin an dakile tashin gobarar, lamarin da ya kai ga lalata kayayyaki na biliyoyin Naira.
- Yanzu-Yanzu: Gobara Ta Tashi A Kasuwar Monday Market A Maiduguri
- Gobara Ta Lalata Kayan N23bn A Wata 3 A Nijeriya —Hukuma
An kai wa ‘yar jaridar hari tare da ma’aikatanta a kokarinta na mika rahoton kai tsaye kan gobarar da ta tashi a kasuwar.
Wani shaidar gani da ido ya ce, ” fusatattun masu shaguna wadanda gobarar ta rutsa da su da kuma masu tausayawa lamarin ne suka farwa ma’aikatan tare da raunata ‘yar jaridar.”
An kai ‘Yar Jaridar Asibitin Sojojin Nijeriya da ke Maiduguri domin karbar magani.