Shugabannin kasashen G-7 sun yi Allah-wadai da harin da Iran ta kai wa Isra’ila, tare da yin kira da a yi sulhu a tsakanin bangarorin.
“Mun yi Allah-wadai da harin da Iran ta kai wa Isra’ila wanda ba mu taba ganin irin sa ba”, a cewar Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Charles Michel.
- Kasar Sin Ta Bayyana Damuwa Game Da Halin Da Ake Ciki Tsakanin Iran Da Isra’ila
- ‘Yansanda Sun Kama Tirelar Sata Da Kayan Miliyan 30 A Bauchi
“Za mu ci gaba da kokari na ganin an yi sulhu. Za mu yi kokarin kawo karshen rikicin Gaza, musamman ta hanyar tsagaita wuta cikin gaggawa.”
Shugabannin sun bayar da cikakken goyon bayansu ga Isra’ila, suna masu cewa a shirye suke su dauki mataki a kan Iran.
“Za mu ci gaba da yin aiki don daidaita lamura da samar da zaman lafiya.
“A halin da ake ciki muna bukatar Iran da wakilanta su daina kai hare-hare, kuma a shirye muke mu dauki matakai da mayar da martani a kanta, ”in ji su, cikin wata sanarwa da shugaban ƙasar Italiya ya wallafa.
A halin da ake ciki, shugabannin kasashen duniya sun bukaci Iran ta tsagaita daga harba makamai masu linzami da ta ke aike wa Isra’ila.
Iran ta kaddamar da hare-hare ga yankin Isra’ila, a matsayin ramuwar gayya kan wani mummunan hari da Isra’ila ta kai ofishin jakadancinta a babban birnin Syria a farkon wannan watan.