• English
  • Business News
Tuesday, October 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ga Dukkan Alamu Japan Ta Zama Butulu

by CGTN Hausa
2 years ago
Japan

FILE - The Fukushima Daiichi nuclear power plant, damaged by a massive March 11, 2011, earthquake and tsunami, is seen from the nearby Ukedo fishing port in Namie town, northeastern Japan, Thursday, Aug. 24, 2023. For the wrecked Fukushima Daiichi nuclear plant, managing the ever-growing radioactive water held in more than 1,000 tanks has been a safety risk and a burden since the meltdown in March 2011. The start of treated wastewater release Thursday marked a milestone for the decommissioning, which is expected to take decades. (AP Photo/Eugene Hoshiko, File)

Zubar da ruwan dagwalon nulikiyar Japan a cikin teku na ci gaba da ɗaukar hankali a duniya yayin da shugabannin ƙasashe makwabta tekun Pacifik suka ci gaba da nuna adawarsu a bayyane a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 78.

Firaministan Tsibirin Solomon Manasseh Sogavare, a yayin da yake gabatar da jawabinsa a babban zauren muhawarar majalisar, ya caccaki ƙasar Japan, da rahoton tantancewa na Hukumar Makamashin Nukiliya (IAEA) ta Duniya game da rashin nuna gaskiya da cin zarafin ƙasashe mazauna yankin Pasifik.

  • “Mafarkina Na Zuwa Sararin Samaniya” 
  • Jarin Da Sinawa ‘Yan Kasuwa Masu Zaman Kansu Ke Zubawa A Angola Na Bunkasa Rayuwar ‘Yan Kasar

Bari mu dan waiwayi baya kaɗan, tarihi ya nuna cewa, shekaru goma sha biyu da suka gabata, bayan haɗarin nukiliyar Fukushima, Japan ta samu taimako daga sassa daban-daban a faɗin duniya. Bayan wadannan shekarun 12, Japan ta yanke shawarar sanya dukkan bil’adama cikin haɗarin gurɓacewar nukiliyarta. Alhalin Yarjejeniya ta shekarar 1972 kan rigakafin gurɓacewar ruwa ta hanyar zubar da sharar gida da sauran al’amura ta hana gurɓata teku, da kuma yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya kan dokar teku ta tanadi cewa ƙasashe na da alhakin kare da kiyaye muhallin ruwa.

Gwamnatin Japan ta fara zubar da ruwan dagwalon nukiliya sama da tan miliyan guda a cikin teku. Mutane da dama sun fusata da wannan yunƙuri, ciki har da gwamnatoci da dama, waɗanda a hankali suna ganin wannan zaɓi a matsayin cin amanar al’umma da wulakanta amincin duniya.

Baya ga yin watsi da bayanan kimiyya, shawarar ta kuma keta dokar ruwa ta ƙasa da ƙasa da kuma ‘yancin ɗan Adam na mutanen Japan da Pacifik, musamman ma damuwar masunta.

LABARAI MASU NASABA

An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu

Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona

Duk da damuwar al’ummar cikin gida da na ƙasa da ƙasa, Japan ta dage kan yin amfani da tekun Pasifik a matsayin “wurin zuba shararta” ta hanyar zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin tekun.

A daidai wannan gaɓar sai mu gabatar da wasu tambayoyi masu muhimmanci. Shin na’urorin tsarkake ko tsaftace tekun na Japan zasu ci gaba da yin aiki da kyau cikin shekaru talatin masu zuwa? A lokacin da ruwan dagwalon da ta zuba cikin tekun ta wuce iyakar mizani? Shin za a iya sanar da al’ummar duniya cikin gaggawa? Menene illar da wannan gubar zata yi wa teku na dogon lokaci akan tsaro da abinci, da lafiyar ɗan Adam, da yanayin ruwa? Rahoton Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) bai bayar da amsar wadannan tambayoyi ba.

Bugu da ƙari, gwamnatin ƙasar Japan na da niyyar sake kunna wutar lantarki da ƙarin makamashin nukiliya duk da alamun girgizar ƙasa da hatsarin tsaro, da bala’in nukiliyar da ke gudana, da kuma ɗimbin kuɗaɗen jama’a da ake buƙata. Bayan sanin cewa halin gaggawar da yanayin duniya ke ciki na buƙatar amintattun hanyoyin samar da makamashi mai tsafta, kamar iska da hasken rana, wadanda dabarun makamashi na gwamnatin ƙasar na yanzu ba za su iya samarwa ba.

A matsayin muhimmiyar hanyar kasuwancin duniya, Tekun Pasifik gida ne ga dukkan ƙasashen yankin. Dan Adam na iya fama da gurɓacewar tekun Pasifik, tare da sakamako mai illa. Kafin Japan ta yi wannan mummunar yunƙurin, an yi fatan hukumar ta IAEA za ta ɗauki ƙarin lokaci tare da zurfafa bincike, da yin la’akari da dukkan abubuwan da za su iya haifar da haɗari.

Dole ne dukkan gwamnatoci da ƙasashe da ke da alhakin sake tantance tasirin wannan mummunar shawarar ga bil’adama su farga. Kira anan ita ce a gudanar da bincike na biyu a cikin hanyar da ta dace kuma a kai ga yanke shawara mafi aminci ga bil’adama.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu
Daga Birnin Sin

An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu

October 28, 2025
Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona
Daga Birnin Sin

Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona

October 28, 2025
Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin
Daga Birnin Sin

Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin

October 28, 2025
Next Post
Xi

Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Taron Tattauna Dauwamammen Ci Gaban Aikin Sufuri

LABARAI MASU NASABA

JIBWIS Ta Miƙa Takardar Koke Ga Gwamnatin Kaduna Kan Zargin Wasu Malamai Da Yunƙurin Tada Husuma

JIBWIS Ta Miƙa Takardar Koke Ga Gwamnatin Kaduna Kan Zargin Wasu Malamai Da Yunƙurin Tada Husuma

October 28, 2025
An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu

An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu

October 28, 2025
Zamfara Ta Fara Sauyawa Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal

Zamfara Ta Fara Sauyawa Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal

October 28, 2025
Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona

Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona

October 28, 2025
Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Ajali Tare Da Jikkata Wasu A Gombe

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Ajali Tare Da Jikkata Wasu A Gombe

October 28, 2025
Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin

Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin

October 28, 2025
Kano Ta Bai Wa Mata 5,200 Tallafin Naira Miliyan 260

Kano Ta Bai Wa Mata 5,200 Tallafin Naira Miliyan 260

October 28, 2025
An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas

An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas

October 28, 2025
Gwamna Bago Ya Amince Da Biyan Karin Albashin Naira 20,000 Ga Ma’aikata 

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Hutun Kwanaki 2 Don Zaɓen Ƙananan Hukumomi

October 28, 2025
Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika

Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika

October 28, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.