A ranar Larabar da ta gabata ne, harajin kashi 25 na shugaban Amurka Donald Trump kan duk wasu kayayyakin karafa da goron ruwa ya fara aiki. Inda Kanada ta mayar da martani kai tsaye da harajin kashi 25 kan kayayyakin Amurka na sama da dala biliyan 20, wadanda suka hada da karafa, kwamfutoci da kayan wasanni. EU ita ma mayar da martani da haraji kan kayayyakin Amurka na kusan dala biliyan 28, wanda zai fara aiki a ranar 13 ga Afrilu.
Hasashen dake tattare da manufar Trump shi ne, idan farashin kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen waje ya tashi a dalilin karin haraji, to za a maida hankali kan kafa masana’antun cikin gida dake samar da irin wadannan kayayyaki, ta hakan za a samu karin ayyukan yi a Amurka. Sai dai Trump ya manta cewa, tsarin karin harjin kwastam na iya zama takobi mai kaifi biyu idan aka yi amfani da shi ba bisa ka’ida ba, kuma zai iya raunata wanda ke rike da shi. Wannan takobin a hannun Trump, yana barazanar zama “makamin lalata huldar cinikayya tsakanin kasa da kasa,” yayin da hakan ke mummunan tasiri ga tattalin arzikin Amurka.
- Layin Dogo Na Habasha-Djibouti Na Habaka Kasuwanci Da Karfafa Hada-hadar Kayayyaki
- Gwamnatin Kano Ta Umarci Ma’aikatanta Da Su Tantance Allbashin Watan Maris Kafin A Biya Su
Sanin kowa ne cewa Amurka ba za ta iya farfado da tsarin samar da kayayyaki da masana’antunta da suka dade da bacewa a cikin dare guda ba, zai dauki watanni ko ma shekaru kafin a sake fasalin tsarin samar da kayayyaki da masana’antunta, duk da cewa masu sayayya na Amurka sun riga sun tsunduma cikin matsalar hauhawar farashin kayayyaki na yau da kullum, sakamakon matakin kara haraji na Trump.
Bisa ka’ida, Trump yana da shekaru hudu ya cimma manufarsa, amma a aikace, lokacin ya yi kadan da zai gamsar da masu sayayya na Amurka. Idan har wannan manufar ta ci gaba da kasancewa a cikin watanni masu zuwa, to tabbas jama’a za su janye goyon bayansu ga shugaban, hatta a tsakanin ‘yan jam’iyyar Republican Congress, wadanda ya dogara da su wajen aiwatar da sabbin dokoki. Idan har suna ganin damar saken zabarsu na cikin hadari a zaben tsakiyar wa’adi na badi saboda tsarin tsuke bakin aljihu da matakin kara kudin fito da ya aiwatar, za su iya yin watsi da goyon bayan da suke baiwa shirin shugaban kasar. Tuni dai ana samun karuwar damuwa daga ’yan kasuwa, musamman wadanda suka dogara da tsarin samar da kayayyaki na duniya wanda manufar kudin fito ta Trump ta kawo ma cikas. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp