Tsohon Firaministan Kenya, Raila Amolo Odinga, zai gana da Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Ahmad Lawan, a Abuja ranar Litinin.
Ana sa ran Odinga zai iso Nijeriya a ranar Lahadi mai zuwa gabanin taron shekara-shekara na kamfanin LEADERSHIP da yake bada lambar yabo karo na 14 inda zai kasance babban mai jawabi.
Odinga, wanda ya wakilci mazabar Lang’ata a majalisar dokokin Kenya, kuma ya rike mukamin Firaministan kasar daga shekarar 2008 zuwa 2013, zai tattauna da Lawan gabanin taron da kamfanin jaridar LEADERSHIP zai yi a ranar Talata mai zuwa.
Taron na LEADERSHIP da bayar da kyaututtuka na shekara-shekara za a gudanar da shi ne a cibiyar taron kasa da kasa da ke Abuja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp