“Ba za a samu ci gaba ba tare da mata ba, kuma dole ne kowa ya amfana da alfanun da hakan zai kawo”, cewar Shugaban kasar Sin Xi Jinping, yayin taron shugabannin duniya kan daidaiton jinsi da karfafa gwiwar mata, a hedkwatar MDD dake birnin New York na Amurka a ranar 27 ga watan Satumban 2015. Hakika, tun daga shekarar 2012, kasar Sin ta fara ba da matukar muhimmanci ga raya harkokin da suka shafi mata, kuma tana tabbatar da mata samun ’yancinsu na demokradiyya, da shiga ana damawa da su cikin harkokin raya tattalin arziki da zamantakewa da kuma cin gajiyar sakamakon gyare-gyare da ci gaban kasa bisa daidaito da tanadin shari’a.
Cikin shekaru 10 da suka gabata, Sinawa mata sun yi kokarin shiga muhimman ayyuka da zama jakadun wayewar kai da kuma jagorori wajen cimma burikansu ta sabbin hanyoyi.
Kafa dokoki masu dace
Wang Xiling, wadda ta samu lambar yabo ta kasa a cikin aikin yaki da talauci, ta ce “abu mafi muhimmanci shi ne, tsayawa da kafarka.” A lokacin da ta sauya daga ’yar kauye mai fama da talauci, zuwa shugabar kungiyar gammaya kan aikin gona, ta gano cewa, ta cimma burinta na zama ’yar kasuwa ne saboda damammakin da sabon zamani ya gabatar.
Tun bayan taron wakilan JKS na 18 da aka yi a shekarar 2012, muhimmin umarnin da shugaba Xi ya bayar kan mata da ayyukan matan, ya saita alkiblar ci gaban harkokin mata a kasar Sin, musamman a sabon zamani.
An rubuta alkawarin nacewa ga manufar kasar ta tabbatar da daidaiton jinsi da kare halaltattun hakkoki da muradun mata da yara, cikin rahotannin tarukan wakilan jam’iyyar karo na 18 da na 19.
Haka kuma, shawarar da aka yanke yayin zama na hudu na taron kwamitin tsakiya na JKS karo na 19, ta jaddada kudurin jam’iyyar na daukakawa da inganta tsare-tsare da dabarun inganta daidaiton jinsi da ci gaban harkokin mata ta kowacce fuska. Kudurin kwamitin tsakiyar jam’iyyar kan manyan nasarori da gogewar da jam’iyyar ta samu cikin shekaru 100 da suka gabata, ya nanata kudurin jam’iyyar na taimakawa wajen karfafa zumunci tsakanin iyalai da akidu da al’adu, da kuma kyautata kare hakkoki da muradun mata da yara.
Shirin raya tattalin arziki da zamantakewar kasa na shekaru biyar-biyar karo na 13, tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020, da irinsa karo na 14 da yanzu ake aiwatar da shi tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025, sun kunshi shirye-shiryen inganta harkokin mata da yara da iyalai, kuma wadannan shirye-shirye sun taimaka wajen shimfida tubali mai kwari na inganta ci gaban harkokin mata, wadanda suka yi daidai da na raya tattalin arziki da zamantakewa.
Kwamitin kula da harkokin mata da yara karkashin majalisar gudanarwar kasar Sin ya tsara wani shirin kasa, na raya harkokin mata tsakanin shekarar 2021 zuwa 2030, inda kwamitin ke saita wasu muradu da dabarun raya harkokin mata a fannonin kiwon lafiya da ilimi da tattalin arziki da sauran wasu fannoni. Kwamitin mai kula da mata da yara a dukkan matakai, ya inganta aiwatar da wannan shiri. An kuma karfafa dabarun inganta harkokin mata wadanda suka kunshi jagorancin kwamitocin jam’iyyar, da hakkokin da suka rataya a kan gwamnatoci, da hadin gwiwa tsakanin kwamitocin kula da yara da mata, da sauran sassan gwamnati, tare da damawa da dukkan kungiyoyin al’umma.
Kasar Sin ta yi ta karfafa harkokin shari’a da suka shafi daidaiton jinsi da hakkoki da muradun mata. Ta kuma kafa wani tsarin shari’a, wanda ya kunshi dokoki da ka’idoji 100, domin su ba da cikakkiyar kariya ga hakkoki da muradun mata. Sabuwar dokar da ake kira da Civil Code, wadda ta fara aiki a ranar 1 ga watan Janairun 2021, ta jaddada ba mata kariya a gidajen aure da kuma cikin iyali.
Dokar hana cin zarafin mata ta kasar Sin, wadda ta fara aiki a ranar 1 ga watan Maris din 2016, ta kare hakkokin mata a cikin iyali. Dokar inganta ilimantar da iyali ta kasar Sin, wadda ta fara aiki a ranar 1 ga watan Janairun 2022, ta bayyana cewa, gwamnati da makarantu da al’umma, su bayar da jagoranci da goyon baya ga hidimar ilimantar da iyali.
Ita kuwa dokar yarjejeniyar gonaki a yankunan karkara ta kasar Sin, an yi mata gyaran fuska a shekarar 2018, domin inganta dokokin kare hakkokin mata kan gonaki a yankunan karkara. An kuma kafa dabarar tantance yanayin daidaiton jinsi a matakan kasa da na larduna 31 da yankunan masu zaman kansu ko birane, domin karfafa dokokin kare hakkoki da muradun mata.
Cigaban harkokin mata daga dukkan fannoni
Harkokin mata a kasar Sin ya samu zarafin ci gaba, kuma ya nuna kyakkyawar makoma a cikin shekaru 10 da suka gabata. Kasar Sin ta inganta samarwa mata kiwon lafiya da inshora, tare da taimaka musu shiga ana damawa da su a harkokin raya tattalin arziki da zamantakewa.
Misali, kiwon lafiyar mata ya ingantu sosai, inda matsakaicin tsawon rayuwar mata Sinawa ya kai shekaru 80.88 a shekarar 2022, kuma mace-macen mata yayin haihuwa ya ragu zuwa 16.1 cikin mata 100,000, tun daga shekarar 2021.
A shekarar 2009, kasar Sin ta kaddamar da shirin binciken sankarar mama da ta mahaifa kyauta, ga matan dake yankunan karkara. Zuwa shekarar 2020, shirin ya aiwatar da binciken sankarar mahaifa ga mata kimanin miliyan 130, da binciken sankarar mama ga mata miliyan 64.
Inshorar kula da mata ya ci gaba da ingantuwa. A karshen shekarar 2020, adadin mata da suka shiga cikin inshorar haihuwa ya kai miliyan 103, wanda ya karu da miliyan 49.31 idan aka kwatanta da na shekarar 2010. Baya ga haka, akwai mata miliyan 650 da suke cin gajiyar inshorar kiwon lafiya.
Haka kuma, cikin shekaru 10 da suka gabata, rawar da mata ke takawa a fannin raya tattalin arziki da zamantakewa, na ci gaba da karuwa. Shi Liping, wadda ta yi gadon surfanin gargajiya na kabilar Miao, kuma wadda ta samu lambar yabo ta mata mafiya nagarta ta Sin, ta jagoranci mata wajen fara kasuwanci ko samun aikin yi. Tsakanin shekarar 2000 da 2008, ta tattaro kayayyakin surfanin gargajiya na kabilar Miao, kuma ta kafa wani ayarin masu surfani da kuma kamfanin kayayyakin bude ido na gargajiya na kabilar Miao, a gundumar Songtao ta kabilar Miao mai cin gashin kanta ta lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin.
Adadin mata cikin jimilar ma’aikatan kasar Sin ya kasance sama da kaso 40 cikin shekaru 10 da suka gabata. Mata sun zama muhimmin karfi dake ingiza kirkire-kirkire da kasuwanci. Mata a kasar Sin a yanzu, su ne suka dauki kaso 55 na masu kasuwanci ta intanet. Haka kuma, a shekarar 2021, mata ne suka dauki kaso 45.8 na ma’aikata a bangaren kimiyya da fasaha.
Raya harkokin ilimi ya taimakawa mata cimma burikansu. Da taimakon shirin Spring Bud, da asusun kula da kananan yara da yara ’yan kasa da shekaru 20 na kasar Sin, Yuzhuoma, daga jihar Tibet mai cin gashin kanta dake kudu maso yammacin kasar Sin, ta kammala karatu tun daga matakin firamare zuwa jami’a, inda ta zama sojar sama a rundunar sojin ’yantar da jama’ar kasar Sin, a shekarar 2011.
Bugu da kari, an yi nasarar cike gibin dake akwai wajen karatun tilas tsakanin maza da mata a kasar Sin. Yawan dalibai mata a kwalejoji da jami’o’i a yanzu, ya zarce kaso 50. Yayin da mata ke kara samun ilimi, suna kara samun kwarin gwiwa wajen samun nasarori a rayuwa.
Cikin shekaru 10 da suka shude, mata suna kara shiga ana damawa da su wajen daukar matakai da tafiyar da harkokin kasuwanci da na demokuradiyya a matakan karkara.
Kididdiga ta nuna cewa, wakilai mata a taron majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta NPC karo na 13, sun kai kaso 24.9 bisa dari na jimilar wakilan majalisar, haka kuma mata mambobin majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta Sin ta CPPCC, ya kai kaso 20.4 na jimilar mambobin majalisar. Wa’adin wakilan majalisar NPC na 13 da na majalisar CPPCC na 13, ya fara ne daga shekarar 2018 zuwa 2023. Wannan adadin ya ci gaba da karuwa a bana, har yawan mata ’yan majalisar NPC karo na 14ya kai kaso 26.54 bisa dari.
Haka kuma bayan zabukan mambobin reshen kwamitin JKS na kauye da kuma kwamitin kauye da aka yi a bana, kowanne kauye na da a kalla mace daya a kwamitocin biyu.
Irin wannan kiddidiga na nuna manyan manufofin Shugaba Xi na yin kyakkyawan tasirin da ake muradi. Shugaba Xi ya shaidawa shugabannin duniya yayin wani taro kan daidaiton jinsi da karfafa gwiwar mata cewa, “dole ne mu karfafa karfin mata na taka rawa wajen raya al’ummarsu da tattalin arziki, da inganta karfinsu na daukar matakai da tafiyar da harkoki da taimaka musu wajen zama shugabanni a fannonin siyasa da kasuwanci da ilimi.”
Mata marasa lisaftuwa ne suke yin kyawawan tasiri a cikin al’umma. Misali, bayan shekaru 10 da tafiyarta sararin samaniya, a ranar 5 ga watan Yunin bara, Liu Yang, ’yar sama jannati mace ta farko a kasar Sin, ta koma sararin samaniyar, inda ta shiga kumbon binciken sararin samaniya na kasar Sin wato Tianhe, yanzu kuma ta riga ta dawo doron duniya lami lafiya. A shekarar 2021 ne, Zhang Guimei, malamar da ta kafa makarantar sakandare ta mata zalla ta farko a kasar Sin, tare da taimakawa ’yan mata 2,000 samun ilimin gaba da sakandare, ta samu lambar yabo ta “July 1st
Medal”, wadda ita ce lambar yabo mafi daraja ta JKS. Liu da Zhang, na daga cikin misalan matan kasar Sin a sabon zamani, wadanda ke ci gaba da himmantuwa wajen bayar da gudummawa domin farfado da kauyuka da yin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da kandagarki da dakile annoba da kuma bayar da jagoranci a matakan karkara.
Har yanzu da sauran rina a kaba, don haka, ci gaba da kokari tare, ita ce hanyar samun ci gaba. Sinawa mata, dake zaman tsintsiya madaurinki daya, na kokarin samun ci gaba cikin ruhi mai karfi, kuma suna cimma manyan nasarori a sabon zamani.
(Kande Gao daga sashen Hausa na CMG)