• Leadership Hausa
Sunday, June 4, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bukatar Kare Hare-hare A Kan Likitoci A Sassan Nijeriya

by Sulaiman
2 months ago
in Rahotonni
0
Likitoci
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A halin yanzu ya zama dole asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya su manna sanarwar gargadi ga marasa lafiya da iyalansu na cewa likitoci da ma’aikatan lafiya na da hakkin gudanar da ayyukansu ba tare da tsoron barazana ko tsoron hare-hare a kan su ba a yayin da suke gudanar da ayyukansu na ceto rayukan al’umma. Tabarbarewar al’amarin kai hare-hare a kan likitoci da jami’an kiwon lafiya a kasar nan ya kai ga haka musamman ganin yadda ake kara fuskantar karancin likitoci kasar nan, inda wasu kasashen duniya ke yi wa likitocinmu tayin kudade masu kauri tare da yanayin aiki mai dadin gaske.

Sai kuma ga shi wadanda suka zabi zama a cikin gida don aikin su na ceto rayukan al’umma suna kuma fuskantar hare-hare daga marasa lafiya da iyalansu. A ‘yan watannin nan an samu karuwar hare-haren a kan likitoci daga marasa lafiya da iyalansu da basu gamsu da wani abu da likitocin suka gudanar ba yayin jinyar ‘yan’uwansu ko kuma suna zargin sakacin Likitocin ne ya yi sanadiyyar rasuwar ‘yanuwansu. Daga dukkan alamu hukumomin asibitocin da jami’an tsaro da hukumomin garuruwan da asibitocin suke basu da karfin da za su iya kawo karshen wannan lamarin da yake karuwa a kullum.

  • Kugiza Kaheru: Shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” Na Haifar Da Ci Gaba A Nahiyar Afrika

Rahoton hari na baya-bayan nan ya faru ne ana ‘yan kwanaki kadan a shiga sabuwar shekarar nan a asibitin koyarwa na Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara inda wasu iyalan mara lafiya daya mutu suka farmaki daya daga cikin likitocin asibitin abin da ya sa hukumar asibitin ta kwace gawar danuwan mutanen. Dalilin da mutane suka bayar na kai wa Likitan harin shi ne wai sakacinsa ne ya kai ga rasuwar danuwan nasu.

Hukumar asibitin ta nemi a tabbatar da hukunta mutanen da suka aikata wannan laifin yayin da kuniyar Likitocin asibitin suka yi yajin aiki na kwana biyar, amma daga dukkan alamu hare-haren na cigaba da aukuwa babu wata alama ta yiwuwar dakatar da dabi’a marakyau.

A bayaninsa, shugaban kungiyar likitoci na Jihar Kwara, Dakta Ola Ahmed, ya ce, a halin yanzu ire-iren wadanan hare-hare yana faruwa a kusan duk mako a sassan jihar abin da kuma yake zama tashin hankali ga likitoci da sauran ma’aikatan lafiya. A wani rahoto irin wannan lamarin ya faru a watan Fabrairu na shekarar 2022 a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Akure ta Jihar Ondo, dan’uwan wani mara lafiya ne ya yi wa wani Likita dukan kawo wuka.
A wani al’amarin kuma, Shugaban Kungiyar Likitoci reshen Jihar Bauchi, Dakta Adamu Sambo a taron manema labarai da aka yi a watan Yuli na shekarar 2022, ya bayyana yadda aka kai wa wani Likita hari, inda yake cewa, “A ranar 8 ga watan Yuli na shekarar 2022, Dakta Mohammed Sani, wanda babban jami’in asibitin ne a Babban Asibitin garin Misau, a yayin gudanar da aikinsa wani danuwan mara lafiya ya kai masa hari da gatari da nufin kashe shi, ba zamu amince da wannan haukar a aikin mu na ceto rayuwar al’umma ba.”

Labarai Masu Nasaba

Shanuna Sun Fi Saukin Kiwo A Kan Mulkin Nijeriya – Buhari

Nijeriya Ce Ta 37 A Kasashen Da Suka Fi Fama Da Ciwon Siga -Kididdiga

“Koma menene koken mutane, ya kamata su mika kukan ne ga hukumar da ta dace maimakon daukar doka a hannunsu. Wannan mutumin ya shigo ba tare da sanin halin da ake ciki ba ya kama wani likitan ma da baya cikin wadanda suka yi jinyar dan’uwan nasa ya shiga saransa da gatari har sau hudu.”

Haka kuma a watan Agusta na shekarar data gabata, iyalan wata mara lafiya sun kai ma wani likiitan mata hari inda suka ji masa mummunan ciwo a kansa, kungiyar likitoci ta yankin Abuja sun nuna damuwarsu a kan hare-hare a kan likitoci da dukkan ma’aikatan lafiya a yankin dama kasar gaba daya.”

Kungiyar ta bayyana damuwarta musamman a kan sabbin likitoci dama wadanda suka tsufa in aka lura da yadda aka cusa lamarin hare-haren a asibitocinmu a ‘yan shekarun nan.

Wadannan hare-haren kamar yadda suke faruwa a Nijeriya yana nuna irin halin takaicin da al’umma ke ciki ne a Nijeriya a kan haka yakamata a nemo kwararru a bangaren kula da mutane masu fushi don a wannan lokacin kusan duk wanda ka taba zaka ga yana cikin fushi ne.

Tabbas ana fuskantar halin talauci, ga kuma tashin hankalin da harkokin ‘yanta’adda masu garkuwa da mutane suka dorawa al’umma da kuma halin tashin hankali da jami’an tsaronmu ke jefa mutane a ciki, lamarin yana matukar shafar tunanin al’umma, daga ka taba mutum sai kawai ya fashe maka. Bayan tabbatar da ganin an hukunta masu kai wa likitoci hari ya kamata hukumomin asibitocinmu su samar da yanayin bayar da shawarwari da magungunan warkar da damuwa ba wai kawai ga marasa lafiya ba har ma da iyalansu da masu jinyar marasa lafiyar gaba daya, musamman ganin wasu ‘yan’uwan basu iya fuskantar labarin mutuwar ‘yanuwansu, su kuma kyautata mu’amalarsu da iyalan marasa lafiya.

A matsayinmu na gidan jarida muna sane da sakaci da rashin iya aiki na wasu likitoci da ma’aikatan lafiya wanda hakan yakan kai ga rasa rayuwar marasa lafiyar da suke jinya. Kamar kowanne lokaci ba a kai ga hukunta su, a kan haka muke kira ga mahukuntan asibitoci su samar da kafar da iyalan marasa lafiya za su iya kai koke a kan likitoci da ma’aikatan lafiya a cikin gaggawa a kuma tabbatar da an yi cikakken bincikre tare da hukunta wanda aka a samu da laifi, wannan zai matukar taimaka wa tare da kwantar da hankalin iyalan marasa lafiya, rashin wannan ne yake haifar da daukar doka a hannun su.

ShareTweetSendShare
Previous Post

Gagarumin Ci Gaban Da Mata Suka Samu A Kasar Sin

Next Post

Duk Da Yarjejeniyar Zaman Lafiya: Rikicin Zabe Ya Lakume Rayukan Mutane Da Dama

Related

Shanuna Sun Fi Saukin Kiwo A Kan Mulkin Nijeriya – Buhari
Rahotonni

Shanuna Sun Fi Saukin Kiwo A Kan Mulkin Nijeriya – Buhari

18 hours ago
Nijeriya Ce Ta 37 A Kasashen Da Suka Fi Fama Da Ciwon Siga -Kididdiga
Rahotonni

Nijeriya Ce Ta 37 A Kasashen Da Suka Fi Fama Da Ciwon Siga -Kididdiga

1 day ago
Yadda Mohammed Bello Koko Ya Tsaftace Hukumar Tashoshin Ruwan Nijeriya
Rahotonni

Yadda Mohammed Bello Koko Ya Tsaftace Hukumar Tashoshin Ruwan Nijeriya

2 days ago
Yadda Amurka Ta Yi Kokarin Amfani Da Nukiliya Wajen Tarwatsa Wata
Rahotonni

Yadda Amurka Ta Yi Kokarin Amfani Da Nukiliya Wajen Tarwatsa Wata

5 days ago
Yadda Cutar Hawan Jini Ke Kisan Mummuke A Nijreriya
Rahotonni

Yadda Cutar Hawan Jini Ke Kisan Mummuke A Nijreriya

7 days ago
Wata Kungiyar Siyasa Ta Yi Allah Wadai Da Rusau A Jihar Kaduna
Rahotonni

Ragargazar Sallama Da El-Rufa’i Ke Yi A Kaduna

1 week ago
Next Post
Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Duk Da Yarjejeniyar Zaman Lafiya: Rikicin Zabe Ya Lakume Rayukan Mutane Da Dama

LABARAI MASU NASABA

Farashin Tumatir Ya Karye Bayan Ghana Da Kamaru Sun Turo Shi Kasuwannin Nijeriya

Farashin Tumatir Ya Karye Bayan Ghana Da Kamaru Sun Turo Shi Kasuwannin Nijeriya

June 4, 2023
Shanun Buhari Sun Ragu Saboda Yawan Kyautarsa — Garba Shehu

Shanun Buhari Sun Ragu Saboda Yawan Kyautarsa — Garba Shehu

June 4, 2023
Babu Gaskiya A Labarin Mutuwar Akeredolu -Gwamnatin Ondo

Babu Gaskiya A Labarin Mutuwar Akeredolu -Gwamnatin Ondo

June 3, 2023
Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Tsarin Wayewar Kan Kasar Sin Mai Dacewa Da Zamani

Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Tsarin Wayewar Kan Kasar Sin Mai Dacewa Da Zamani

June 3, 2023
Ziyarar Shugaba Xi Jinping A Wuraren Al’adun Sin Tana Da Babbar Ma’ana

Ziyarar Shugaba Xi Jinping A Wuraren Al’adun Sin Tana Da Babbar Ma’ana

June 3, 2023
Sin Ta Jaddada Kira Ga Sassan Masu Ruwa Da Tsaki A Rikicin Sudan Da Su Gaggauta Dakatar Da Bude Wuta

Sin Ta Jaddada Kira Ga Sassan Masu Ruwa Da Tsaki A Rikicin Sudan Da Su Gaggauta Dakatar Da Bude Wuta

June 3, 2023
Rashin Lafiyar Maigidana Ne Babban Tashin Hankalin Da Na Fuskanta A Vila – Aisha Buhari

Rashin Lafiyar Maigidana Ne Babban Tashin Hankalin Da Na Fuskanta A Vila – Aisha Buhari

June 3, 2023
‘Yan Bindiga Sun Kai Wa Ayarin Yahaya Bello Hari, Sun Raunata Jami’an Tsaro

‘Yan Bindiga Sun Kai Wa Ayarin Yahaya Bello Hari, Sun Raunata Jami’an Tsaro

June 3, 2023
Shugaban Eritrea Da Takwaransa Na Congo Kinshasa Sun Yabawa Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

Shugaban Eritrea Da Takwaransa Na Congo Kinshasa Sun Yabawa Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

June 3, 2023
Wane Ne Sabon Kocin Chelsea Mauricio Po-chettino?

Wane Ne Sabon Kocin Chelsea Mauricio Po-chettino?

June 3, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.