Ministan da Shugaba Bola Tinubu ya zaba a matsayin minista, Abbas Balarabe, wanda ya fadi a lokacin da ake tantance shi a majalisa, ya yi karin haske kan batun lafiyarsa.
Balarabe ya bayyana cewa ya gaji ne a lokacin da ake tantance shi a matsayin minista.
- Tattalin Arzikin Afirka Zai Durkushe – Bankin Duniya
- Takardun Karatun Tinubu Ba Na Bogi Ba Ne – Fadar Shugaban Kasa
A cewar Balarabe, a ranar Talata ne aka sanar da shi nadin nasa, kuma ya kwana yana shirin game da ranar wanda hakan ya sa bai samu hutu ba.
Ministan ya ce, “Gaskiya gajiya ce. Na samu labarin zaba ta a jiya sai na fito daga Kaduna.
“Akwai abubuwa da yawa da zan yi wadanda na halarta cikin dare.
“Abin da ya faru a yau ya faru ne sakamakon tsantsar gajiya.
“Ina son na gode wa Majalisar Dattawa bisa fahimtarsu musamman Sanatocin Jiha ta (Kaduna) wadanda duk suka taru tun jiya tare da tawagar likitoci suka kula da ni.
“Ina cikin lafiya yanzu, babu abin da ke damuna. Abin da na fuskanta shi ne gajiya wanda zai iya faruwa ga kowa. ”
An ga yadda aka yi fama a majalisar dattawa, yayin wanda ya maye gurbin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya fadi kwatsam lokacin da ake tantance shi.
Balarabe, wanda shi ne mutum na biyu da aka zaba da aka tantance bayan Dokta Ibrahim, ya kammala bayyana abubuwan da ya faru a lokacin da lamarin ya faru.