Mohamad Ali Mohd Shalabi, ‘dan kasuwa ne daga kasar Jordan, wanda ke gudanar da dakin cin abinci a birnin Yiwu na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin. Ya isa lardin Zhejiang ne a shekarar 2002, a wancan lokaci, yana son kafa wani kamfani ne a wurin.
A watan Yunin shekarar 2014, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba yin bayani game da aikin da Mohammed ya gudanar, a dandalin taron da aka shirya tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa, inda ya bayyana cewa, “Wani saurayi dan kasar Larabawa yana yin kokari matuka domin cimma burinsa kamar yadda Sinawa suke yi, lamarin da ya shaida haduwar burikan kasar Sin da na kasashen Larabawa.”
Mohamad ya zana hoton shawarar ziri daya da hanya daya a kan bangon dakin cin abincinsa, domin nuna babbar godiyarsa ga shugaba Xi, inda ya yi tsokaci da cewa, “Wata kasa mai bude kofa ga ketare ta samar da damammaki da dama ga ‘yan kasashen waje, a sanadin haka, na cimma burina.” (Mai fassara: Jamila)