Bisa gayyatar da shugaban kasar Amurka Joe Biden ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai tafi birnin San Francisco na kasar Amurka cikin kwanaki masu zuwa, don ganawa da shugaba Biden, gami da halartar kwarya-kwaryar taro karo na 30 na shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki a yankin Asiya da tekun Pasific (APEC). Wannan ziyara ce da shugaban na kasar Sin zai sake kai wa kasar Amurka, bayan wasu shekaru 6, kana sake ganawar da shugabannin Sin da Amurka za su yi bayan shekara 1, wadda ke da ma’anar musamman.
Wani abun lura shi ne, wasu kwanaki da suka gabata, kungiyar makada ta Philadelphia Orchestra ta kasar Amurka ta zo kasar Sin don halartar biki. Wannan kungiyar makada ita ce kungiyar makada ta kasar Amurka ta farko da ta ziyarci kasar Sin, bayan kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, inda ta taimaka wajen farfado da cudanyar kasashen Amurka da Sin a fannin al’adu. Daga nan, kungiyar ta ziyarci kasar Sin har sau 12, inda ta taka muhimmiyar rawa a kokarin kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2. Sai dai a wannan karo, shugaba Xi Jinping ya amsa wata wasika ta shugaban kungiyar makada ta Philadelphia Orchestra Matias Tarnopolsky, inda ya ce, yana fatan ganin makadan kungiyar sun hada gwiwa tare da takwarorinsu na kasar Sin, da na sauran kasashe, don karfafa cudanya, da raya fasahohi na al’adu, ta yadda za a ci gaba da tabbatar da cudanyar kasashen Sin da Amurka a fannin al’adu, da kasancewar zumunta tsakanin al’ummun kasashe daban daban. Wasikar shugaba Xi ta nuna yadda ake son karfafa cudanya da zumunta tsakanin Sin da Amurka, wadda ta nuna wani yanayi mai yakini kan ganawar shugabannin kasashen Sin da Amurka.
- Kade-Kaden Symphony Ta Philadelphia Na Ba Da Gudummawa Waje Inganta Abokantakar Dake Tsakanin Sin Da Amurka
- Ana Begen Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka A Birnin San Francisco
A dayan bangare kuma, mu’ammalar gwamnatocin Sin da Amurka ita ma ta samu ci gaba mai armashi a kwanakin nan. Bisa gayyatar da ministar kudi ta kasar Amurka Janet Yellen ta yi, He Lifeng, mataimakin fitaministan kasar Sin, wanda ke jagorantar aikin musayar ra’ayi tare da bangaren Amurka ta fuskar tattalin arziki da ciniki, ya ziyarci kasar Amurka tsakanin ranar 8 zuwa ta 12 ga watan Nuwamban da muke ciki, inda ya tattauna tare da Madam Yellen, gami da cimma matsaya kan wasu batutuwa. Misali, kasashen 2 sun yarda da kara musayar ra’ayi da juna, don neman samun matsaya daya, da shawo kan bambancin ra’ayi. Kana sun jaddada cewa ba za su katse hulda a fannin tattalin arziki ba. Haka zalika, sun yarda da yin kokari tare don tinkarar wasu kalubaloli na bai daya, irinsu tabbatar da karuwar tattalin arziki, da samun wani yanayi mai karko a fannin hada-hadar kudi, da dai sauransu. Yadda aka cimma matsaya a wadannan fannoni shi ma ya nuna cewa an share fage sosai domin ganawar da za a yi tsakanin shugabannin kasashen Sin da Amurka.
Da ma huldar dake tsakanin Sin da Amurka ta gamu da matsala, tun bayan da kasar Amurka ta fara takaita cinikin da take yi da kasar Sin bisa kashin kanta a shekarar 2018, lamarin da ya sa gamayyar kasa da kasa damuwa kan yiwuwar abkuwar “sabon yakin cacar baka”. Amma a hakika, matakan da kasar Amurka ta dauka ba su dace da moriyar jama’ar kasar ba, saboda babbar moriyar kasashen 2 a hade suke, wato suna bukatar juna. Wannan ya yi kama da maganar da Gavin Newsom, gwamnan jihar California ta kasar Amukra ya fada, yayin da yake ziyara a kasar Sin a kwanan baya, inda ya ce, “ Idan kasar Sin ta samu karin nasarori, to, mu ma za mu cimma karin nasarori. ”
Ban da haka, kasashen Sin da Amurka su ne masu tattalin arziki mafi girma a duniya, inda adadin tattalin arzikinsu ya zarce kashi 1 cikin kashi 3 na tattalin arzikin daukacin duniya. Saboda haka gwamayyar kasa da kasa na son ganin huldar dake tsakanin Sin da Amurka ta koma cikin wani yanayi mai armashi, ta yadda za a iya samar da sauki ga mawuyacin halin da duniya ke ciki, da tabbatar da kwanciyar hankali, da ci gaban tattalin arzikin mabambantan kasashe. Ta hanyar ganawar da shugabannin Sin da Amurka za su yi a wannan karo, ana sa ran ganin huldar dake tsakanin kasashen 2 ta inganta, lamarin da zai biya bukatun kasashen duniya.
Sai dai don cimma burin kyautata huldar dake tsakanin Sin da Amurka, ana bukatar kasar Amurka ta cika alkawarin da take dauka, maimakon yadda ta saba yi a baya, inda take fadin wani abu ga kasar Sin, amma ta aikata wani abu na daban daga bisani. Kamar yadda Gal Luft, darektan cibiyar nazarin aikin tsaro na duniya, ya fada: Karfafa cudanya tsakanin Sin da Amurka zai taimakawa daidaita huldarsu, domin ana bukatar aiwatar da sakamakon da aka cimma. (Bello Wang)