Mataimakin shugaban jami’ar gwamnatin tarayya da ke karamar hukumar Dutsen Ma a Jihar Katsina (FUDMA), Farfesa Arma Ya’u Bichi ya bayyana cewa yunkurin Shugaban kasa, Sanata Asuwajo Bola Ahmad TInubu na yin gwamnatin hadika alkairi ce.
A cewarsa, Ganawar Tinubu da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso za ta kasance alkairi ga Nijeriya, domin shi Kwankwaso yana kishin al’umma da daukacin mutanen Nijeriya gaba daya.
- Daular Sakkwato Ta Buga Littattafan Malaman Musulunci Miliyan 3.2 —Sarkin Musulmi
- Adadin Motocin Da Aka Sayar Zuwa Ketare Ya Karu Da 58.7% A Watan Mayu
Farfesa Arma Ya’u ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a ranar Asabar da ta gabata.
Har ila yau, Farfesa Arma Ya’u ya yi kira ga daukacin al’ummar Nijeriya kan su ba da hadin kai da gwamnatin tarayya dama gwamnatin Jihar Kano a karkashin shugabancin Injiniya Abba Kabir Yusuf domin ci gaban Kano da ma Nijeriya baki daya.
A karshe ya ce shiri ko tsari na raba mukamai ga ‘yan Nijeriya daga sassa daban-daban na kasar abun ne mai kyau kowa ya ji ana yi da shi a tafiyar da mulkin Nijeriya domin bayar da gudmmawar kowa da kowa a Nijeriya.