Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa ganawarsa da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ta yi amfani.
Shugabannin biyu sun gana yayin wata liyafar cin abinci ta musamman a fadar Élysée Palace, da ke Paris, a ranar 10 ga watan Satumba, 2025.
- Amfani Da Karfin Tuwo Ba Zai Iya Kawo Zaman Lafiya A Yankin Gabas Ta Tsakiya Ba
- Mataimakin Shugaban Unilever: Mun Kudiri Aniyar Zama “Masu Tseren Gudun Fanfalaki” A Kasar Sin
Sun tattauna hanyoyin ƙara haɗin gwiwa tsakanin Nijeriya da Faransa don ci gaban juna da zaman lafiya.
Tinubu dai yana hutun kwanaki 10 na aiki, inda zai kwashe lokaci a Faransa da Birtaniya.
Wannan tafiya ta biyo bayan ziyarar aiki da ya kai Japan da Brazil a watan Agustan 2025.
Wannan shi ne karo na biyu da Tinubu ya ziyarci Faransa cikin watanni shida, bayan ziyararsa ta baya a watan Afrilu 2025.
Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa tafiyar ta kasance wani ɓangare na hutun shekara-shekara, ba don abin da ya shafi lafiyarsa ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp