Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje na kara shan matsin lamba a kan ya sauka daga mukaminsa, inda wani jigon APC, Alhaji Saleh Zazzaga ya rubuta masa wasika tare da ba shi wa’adin kwanaki 7 ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban jam’iyyar APC.
Alhaji Zazzaga, ya kasance shugaban kungiyar ‘ya’yan jam’iyyar APC na yankin arewa ta tsakiya, sannan kuma shi mamba ne a lokacin yakin neman zaben Tinubu/Shettima, ya dai bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Jos, Babban Birnin Jihar Filato.
- Janar Gowon: Tsohon Shugaban Kasa Mafi Tsawon Rai A Nijeriya Na Cika Shekara 90
- Majalisa Ta Amince Jami’an Kiyaye HaÉ—urra Su RiÆ™e BindigaÂ
Ya ce a cikin wasikar da ya rubuta akwai dalilansa wanda ya bukaci Ganduje ya yi murabus tare da bayar da wa’adin kwanaki 7 da zai kare a ranar Litinin na mako mai zuwa, wanda ya ce zai dauki matakin shari’a.
A cewarsa, a babban taron jam’iyyar da aka gudanar da ranar 26 ga Maris, 2022, ya kamata a zabi dan yankin arewa ta tsakiya ne ba Ganduje da ya fito daga yankin arewa maso yamma ba.
Jigon jam’iyyar APC ya ce kasancewar Ganduje shugaban jam’iyyar hakan ya saba wa sashi na 31.5 31.5 (i) da (ib) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC na shekara 2022 wanda aka yi wa garanbawul, sannan kuma ya saba wa yarjejeniyar tsarin karba-karba na mukamin shugabancin jam’iyyar wanda ya kamata a bai wa yankin arewa ta tsakiya.
Ya ce wasikar tana zama wani shaida na hanyar warware rikici cikin sauki da kuma tattaunawa ta lumana, amma duk da haka Ganduje ya yi kememe ya ci gaba da zama kan mukamin da ya kamata a bai wad an asalin yankin arewa ta tsakiya.
Haka kuma Zazzaga ya yi kwafin wasikar ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio da shugaban majalisar wakilai, Honorabul Tajudeen Abbas da kwamitin gudanarwa na APC na kasa da kuma sashin shari’a na jam’iyyar APC.
Idan za a iya tunawa dai, kungiyar APC na yankin arewa ta tsakiya sun gurfanar da Ganduje a gaban babban kotun tarayya da ke Abuja na neman a tsige shi daga kan mukaminsa na shugaban jam’iyyar, sai dai kotun ta yi watsi da karar sakamakon wasu dalilai.
Sai dai kuma, ‘ya’yan jam’iyyar APC a yankin arewa ta tsakiya da sauran wasu jiga-jigan jam’iyyar daga yankin sun ci gaba da wannan yaki har sai hakarsu ta cimma ruwa.