Majalisar zartarwa ta jihar Kano, ta amince da sake yin nazari akan kudaden da za kashe don gyran titin garin Kwankwaso da ke a karamar hukumar Madobi.
Majalisar ta amince za yi aikin akan naira biliyan 97.826. An kuma bayar da wannan kwangilar a watan maris na 2022 akan kudi naira miliyan 372.268, inda aka fara bayar da naira miliyan 154.491 wanda aikin a yanzu ya kai kashi 50 a cikin dari.
- 2023: Idan Ka Isa Ka Shirya Tattaki Irin Namu A Kano – Ganduje Ya Kalubalanci Kwankwaso
- 2023: Takarar Peter Obi Za Ta Bai Wa PDP Matsala A Lokacin Zabe – Ganduje
Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, wanda ya sheda wa manema labarai hakan jim-kadan bayan kammala zaman majalisar da ya gudana a gidan gwamnatin jihar, inda ya ce, an yi nazarin ne saboda yadda kayan aikin gine-gine, ke kara tashi sama, inda ya sanar da cewa, ganin karin ne yasa gwamnatin ta sake yin duba akan kwangilar, inda ta mayar da ita zuwa naira miliyan 470. 095.
Garba ya ci gaba da cewa, majalisar ta kuma amince da a fitar da naira miliyan 40.373 don a gyara na’urorin samar da ruwan borehole mai aiki da wutar sola a kasuwanni 10 da ke a karkara.