Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya Jajanta wa Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Alhaji Alkali Usman Baba, bisa gobarar da ta rutsa da wasu ofisoshi a shelkwatar Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano ranar Lahadin data gabata.
Daraktan yada labaran Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Hassan Musa Fagge, ya shaidawa LEADERSHIP Hausa cewa, Gwamnan wanda mataimakinsa kuma dan takarar kujerar Gwamnan Kano, Nasiru Yusif Gawuna, ya wakilta a lokacin ziyarar domin duba irin asarar da aka yi, ya nuna damuwarsa kan faruwar wannan lamarin.
“Mun yi matukar girgiza a lokacin da muka samu labarin wannan annobar gobara, saboda haka muke jajanta maku a madadin Gwamnati da Jama’ar Jihar Kano.”
“Muna fatan za’a dauki matakan kare faruwar irin wannan hadari nan gaba.”
Hakazalika Gwamnan ya yi addu’ar fatan hakan ba zata sake faruwa nan gaba ba, sannan ya bada tabbacin gudunmawa tare da yaba wa kokarin Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano kan shawo kan matsalar gobarar.
A nasa jawabin, Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Kano, Alhaji Mamman Daura, cewa ya yi, yana Ofis lokacin da wutar ta kama. “Muna ci gaba da binciken musabbabin wutar, Sai dai an yi nasara babu asarar rai”
Kwamishinan ya gode wa Gwamnan bisa ziyarar, ya ce hakan ya nuna irin damuwar Gwamnatin Kano kan lamarin.