Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje, ya nada tsohon kwamishinansa na yada labarai da harkokin cikin gida, Muhammed Garba, a matsayin shugaban ma’aikatan Jam’iyyar.
Garba, kwamishina ne a gwamnatin Ganduje na tsawon shekaru takwas da yayi yana gwamnan Kano.
Daya daga cikin hadiman Ganduje kan harkokin yada labarai Abubakar Ibrahim ne ya sanar da nadin Garba.
Garba, Tsohon shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) ne, ya kuma taba rike mukamin sakataren yada labarai na ofishin mataimakin kakakin majalisar wakilai.
‘Yan jarida da kungiyoyin farar hula a Kano sun yaba wa tsohon Gwamna Ganduje bisa wannan nadin, inda suka bayyana Garba a matsayin kwararre wanda ya ke wa al’umma hidima.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp