Tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya taya al’ummar Musulmi murnar Babbar Sallah, inda kuma ya koka da yadda ‘yan jam’iyyar NNPP ke ta rushe ayyukansa da ya kafa a jihar.
A sakonsa na Sallah, wanda ke kunshe cikin wata sanarwa da tsohon kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Malam Muhammad Garba, ya fitar, Ganduje ya ce a daidai wannan lokaci na bukukuwan Sallah, jam’iyyar NNPP ta dakatar da biyan albashin ma’aikata sama da 10,000 da tsohuwar gwamnatin ta dauka aiki a lokacin mulkinta kan wasu dalilai mara sa inganci.
Ganduje ya bayyana cewa, dakatar da albashin wanda ya shafi ma’aikata, musamman malaman makaranta da aka dauka aiki sama da watanni Uku da suka gabata, ya haifar da fargaba a ma’aikatan gwamnatin jihar kan yiwuwar korar ma’aikata a wasu sassan ma’aikatun jihar.
A cikin sanarwar, tsohon gwamnan ya bayyana damuwarsa kan soke karin girma da aka yi wa malaman makaranta da kuma dakatar da biyan albalbashinsu a matakin aikinsu kafin karin girman.
Ganduje ya kuma kara da cewa, matakin da sabuwar gwamnatin ke dauka yanzun, yana nuna shirinta na korar malaman tare da maye gurbinsu da mutanensu.