ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugaban INEC Ya Tafka Aika-Aika Fiye Da Emefiele, Ya Kamata A Kore Shi —Buba Galadima

by Sadiq
3 years ago
INEC

Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi kira ga shugaba Bola Tinubu da ya kori Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).

Ya yi magana ne a cikin wata hira da gidan talabijin na Channels.

  • Ganduje Ya Yi Allah-wadai Da Dakatar Da Albashin Ma’aikatan Da Gwamnatinsa Ta Dauka
  • Tinubu Na Bukatar Addu’a —Gbajabiamila

Galadima ya zargi shugaban INEC da yin zagon kasa ga ‘yan Nijeriya a zaben shugaban kasa da ya gabata.

ADVERTISEMENT

Ya ce abin da Yakubu ya yi ya fi “zunuban” da Godwin Emefiele, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya aikata.

“Dole ne shugaban INEC ya tafi, abin da ya yi ya fi abin da Godwin Emefiele ya yi. Ya hada baki da wasu mutane domin su muzgunawa ‘yan Nijeriya. Ya aikata laifi mafi girma da kowa zai yi,” in ji shi.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a karkashin Yakubu ta sha suka sosai kan gazawarta na saka sakamakon zabe kamar yadda ta yi alkawari, lamarin da hukumar zaben ta dora alhakin tabarbarewar fasaha.

A wani taron manema labarai da ta gudanar a ranar Talata, tawagar da ke sa ido kan zabuka ta Tarayyar Turai ta ce amincewar da jama’a ke da ita ga hukumar ta yi matukar illa.

Amma da yake mayar da martani, Festus Okoye, ya ce matsalar da aka samu wajen dora sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, bai kamata ya kawar da dukan zaben da aka gudanar a asar baki daya ba.

“Ba daidai ba ne a yi la’akari da dukkan ayyukan hukumar bisa ga kura-kuran da aka samu a sakamakon zaben shugaban kasa,” in ji shi.

Da yake karin haske a hirar ta gidan talabijin, Galadima ya shaidawa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP da kuma Peter Obi na jam’iyyar Labour cewa suna bata lokaci suna kalubalantar nasarar shugaba Bola Tinubu.

Obi da Atiku sun gurfana gaban kotu domin kalubalantar nasarar Tinubu.

Sai dai Galadima, wanda ya yi ikirarin cewa an daura auren ne da kura-kurai, ya kara da cewa sakamakon zaben shugaban kasa da kotuna ba ta taba yin watsi da shi ba tun 1979.

M“Wane dan siyasa ne ya yi nasara a kotu tun 1979 a Nijeriya a karar da ya shigar da shugaban kasa? Me ya sa za mu barnata biliyan 10 ko biliyan 15 saboda mun ji wasu na kashe irin wadannan biliyoyin kudi a shafukan sada zumunta a kotun; idan muna da irin wadannan kudade za mu yi amfani da su wajen shiryawa babban zaben 2027.

“Jam’iyyar NNPP tana da karfi, idan ban da INEC ta goge tambarinmu a wasu jihohi, da mun yi nasara fiye da yadda ake zato,” in ji shi.

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
Dalibai Sun ‘Yantar Da Fursunoni 6 A Gidan Yarin Suleja

Dalibai Sun 'Yantar Da Fursunoni 6 A Gidan Yarin Suleja

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.