Assalamu alaikum, masu karatu, barkanmu da sake haduwa a wannan makon. Za mu karasa batun aure da muke yi kafin daga bisani mu dora da wani darasin.
Kamar yadda muka yi bayani a makon da ya gabata, wata rana, Annabi Dawud, yana cikin dakinsa yana Ibada, sai ga Mutane biyu sun shigo ba tare da masu gadinsa sun sani ba, sai ya razana, ya ce musu ku kuma su waye kuma daga ina, sai daya ya ce “wannan dan’uwana ne, yana da shanu 99, ni kuma ina da daya, amma ya matsa min sai na ba shi ita, dole na ba shi ita sabida ya rinjaye ni a zance ”, bayan Annabi Dawudu ya yi musu hukunci ya tabbatar da cewa mai 99 ya zalumci mai daya sai suka koma.
- Dabarun Kasar Sin Na Kiyaye Yankuna Masu Dausayi Ga Zuriyoyi Dake Tafe
- LEADERSHIP Ta Jinjina Wa Shehu Isma’ila Mai Diwani Kan Shafin Dausayin Musulunci
Nan take, Annabi Dawuda ya fahimci cewa, ya yi wa kansa hukunci ne, sai ya nemi tuba kuma Allah ya gafarta masa.
An karba daga Hadisin Sayyadina Anas, Annabi (SAW) yana cewa, “Allah ya fifita ni a cikin mutane da abu Hudu: 1- Na fi kowa kyauta 2- Na fi kowa sadaukantaka 3- Na fi kowa saduwa da Iyali 4- Na fi kowa iya damka.”
Manzon Allah (SAW) ya fi kowa hakuri amma in ka tabo Allah, za ka gane ya fi kowa iya kai hari. Wata rana Annabi (SAW) ya kai hari kabilar Khaibara, sai ga Annabi (SAW) yana cewa, ‘Allahu Akbar, Karibat khaibara’ Khaibara ta rushe. Duk kabilar da muka wayi gari a cikinta, za ta yi mummunar Asuba.
Amma alfarma ko matsayi, abun alfahari ne da yabo ga masu hankali a al’adar Mutane, a ce wane, Shugaban kasa ne, Gwamna ne, Sarki ne, ko wani Shugabanci dai na daban, alfarmar mutum gwargwadon girmansa a zuciya. Da yawa a kan hada shugaba da waninsa a dakin kwanciya yayin gabatar da aikin Hajji, amma duk ba su san juna ba, yayin da aka gaya masa cewa, abokin kwananka sarki ne ko shugaba sai ka ga girmansa a zuciyarka ya canza sabanin a ce ba shugaba ba ne.
Allah tabaraka wa ta’ala ya fada cikin girmama Annabi Isah (AS), da fadinsa “…Wajihan fid dunya wal akhira, ma’ana Mai girma ne a duniya da lahira”
Sai dai, girma ko matsayi mai cutarwa ne daga tulin jama’a, wani yana amfani da damar ya taimaki tulin Jama’a wani kuma ya azabtar da mutane da matsayin. Sabida haka, wanda ya ki shugabanci, ya samu hujjah a Shari’a amma in za ka amfana ka amfanar, samun matsayin shi ya fi daukaka.
Annabi (SAW), Allah ya ba shi girma da daukaka na a dinga ganin girmansa da darajarsa a zuciya tun kafin Annabta, lokacin jahiliyya da bayan Annabta.
Da yawan lokuta, Kafiran Makkah suna kokarin cutar da Annabi (SAW) da Sahabbansa a bayan idonsa amma da sun hadu da Annabi (SAW) sai su girmama lamarin sa, ba za su iya cutar da shi ba.
Wannan Alhamdu lillah, gadon Annabi (SAW) ne ya bai wa duk masu gaskiya, in ka tsaya wa gaskiya, kullum azzalumai za su yi ta shirin cutar da kai amma in kun hadu ba za su iya ba sai dai su yi ta shiri a bayan idonka.
Hadisai da misalai na hana Azzalumai cutar da Annabi in sun hadu suna da yawa, amma za mu zo muku da wasu daga cikinsu.
Sayyidina Ali yana cewa, idan Mutum ya hadu da Annabi (SAW) a hanya bai san da zuwansa ba, to sai ya razana da yin makerketa sabida ganin sa.
An ruwaito daga wata sahabiya da ake kira Kailatu, yayin da taga Annabi (SAW) sai ta razana ta fara makerketa, sai Annabi (SAW) ya ce mata, “ya ke baiwar Allah, ki nutsu, ni ba kowa ba ne sai dan mace, mai cin kilishi a Makkah.”
A wani hadisin Abi Mas’ud an ruwaito yana cewa “An kawo wani mutumi gaban Annabi (SAW) yana ta makerketa, sai ya ce masa, sauwake wa kanka Malam, ni fa ba sarki ba ne…” Amma duk wannan girmamawa ce da kankan da kai na Annabi (SAW), don shi ne cikamakon Manzonni, Allah ya ba shi karamci da kwarjini a duniya da lahira.
Alhamdu lillah! Wannan babin da muka kammala ya yi nazari kan abubuwan da ake alfahari da karantasu a rayuwa kamar bacci da yawan cin abinci sannan ya yi Nazari a kan abinda ake alfahari da yawaita su, kamar auratayya da daukaka. Duk wanda aka ce masa mai yawan bacci da cin abinci ne, an zage shi! Duk wanda aka ce masa yana da yawan ‘ya’ya da mata, an yabe shi, sai dai in ba shi da halin kula da tarbiyyarsu da ciyar da su.
Abin Da Ake Alfahari Da Su Wajen Daidaito
Wannan bangaren kuma da za mu shiga zai yi duba cikin abin da ake alfahari da su wajen daidaito a cikinsu (wanda hali yake sassabawa).
Ma’abocin dukiya mai yawa a wurin dukkan mutane, abun girmamawa ne, sai dai ‘yan kadan masu hankali a cikin mutane, ba wai za su wulakanta dukiya ba ne, amma so a zuciya irin wanda jahilai ke yi ma duk wanda ke da dukiya, su bayin Allah nasu ba haka ba ne, su ma’abota hankali ba haka suke girmama ma’abocin dukiya ba, suna da irin nasu.
Amma su sauran jama’a ba su da ilimin tantance dukiya, mai dukiya ko waye kawai za su girmama shi, amma malamai suna da ilimin tantance dukiya.
Da yawan jama’a suna girmama masu dukiya ne sabida suna ganin za su iya biya musu bukatunsu na bangaren dukiya, don haka, kudi a kan-kansu ba su da wata falala sai in za su biya bukatar da ake da ita a lokacin. Misali, kana da Naira Miliyan daya (N1,000,000) amma ba zaka iya kashe naira dubu dari (N100,000) ba don biyan bukata. Irin wannan kudin ba su da amfani. Don haka falalar kudi tana kan abin da za ayi da kudin.
Amma in mutum zai yi amfani da kudi ya biya bukatunsa, da bukatun wadanda suka bujiro a gare shi na daga mutane da ‘yan’uwa da abokan arziki, sannan kuma ya bi da kudin ta inda suka dace a bi da su, ana neman taimako ka yi, yin hakan ka siyan ma kanka darajoji masu girma da kirari mai kyau kuma ka gina darajoji masu girma a zukatan mutane, har ta kai ga wata rana ko makiyinka sai ya yabe ka, in har ka samu wannan, kudi ya zama daraja mai girma, kuma mai dukiyar ya zama madaukaki.
Ana cewa, in kana so ka mallaki mutumin kirki, to ka taimake shi. Amma in ka taimaki mutumin banza, shi kuma sai ya ga kaman dole ne a taimake shi.
Duk wanda ya ciyar da kudadensa wajen taimakon mutane, ya nufi Allah sai ka ga ya samu yabo wurin mutanen Allah da na duniya sannan kuma ya sami daraja a gidan duniya da lahira.
Kuma duk wanda ya ciyar da dukiyarsa kan harkar duniya, lallai duniyarsa za ta yi kyau, kamar Turawa da suke ciyar da dukiyarsu kan taimakon marasa karfi na yankin duniya, babu ruwansu da lahira don duniya suka yi, sabida haka, duniyarsu za ta yi kyau. Amma kamata ya yi, wanda shi kuma ya san lahira ya ninka kyutar wanda bai san lahira ba. Wanda ya yi haka, ya sami duniyar da lahirar, masu hankali da marasa hankalin duk za su yabe shi.
Amma duk randa mai kudi ya kasance, shi ba mai son taimako ba ne sai dai kwadayin tara kudin kawai, bai ba wa ‘yan duniyar ba balle su yabe shi, bai ba wa bayin Allah ba ballantana su ma su yabe shi, sai wadannan tulin kudin su zama kamar babu. Kuma in ya tashi mutuwa, sai ya mutu a wulakance sabida bai tsayar da kudin a hanyar da ta dace ba, kai bari ma, ya bi da kudin ta hanyar hallaka. Bai taimaki kowa ba.
Bari dai, duk wanda Allah ya bai wa wadatar arziki bai taimaki kowa ba, arzikin zai jefa shi hali makaskanci, babu mai kallonsa a duniya da lahira sabida bai taimaki mabukata ba.