Wata babbar kotu a Yola, ta yanke hukuncin daurin rai da rai, ga wasu mutane 3 da ta samu da laifin garkuwa da wata mace ‘yar jarida, Amra Ahmad Diska, da ke aiki da gidan Radiyon ABC mallakin gwamnatin jihar.
Alkalin kotun mai shariya Danladi Muhammad, ya kuma daure wasu da su ka yi garkuwa da wata mata shekara 10, ko kuma su biya naira miliyan guda, ya kuma daure wani guda shekaru 5 a gidan mazan ba tare da zabin biyan fansa ba.
Wadanda kotun ta yiwa daurin rai-da-rai sun hada da Muhammad Habib Maki (aka Dram), Barde Usman da Umar Mammanjoda (aka Umar Mbamba).
Haka kuma daga baya kotun da daure Likewise, Husseini Hamman (aka Awilo) shekaru 5, ba tare da zabin biyan tara ba, Umar Abubakar (aka Naibi) kuma zai kwashe shekaru 10 a gidan yari ko kuma biyan tarar naira miliyan daya.
Idan za’a tuna a ranar 4/3/2021 ne, wasu mutane dauke da makamai suka shiga gidan Ahmad Isa Mbamba, a karamar hukumar Yola ta kudu, su ka tafi da matarsa.
Rahotanni sun tabbatar da matar ta kwashe tsawon kwanaki bakwai a hannun mutanen da su ka yi garkuwa da ita, inda su ka saketa bayan da aka biyasu naira miliyan 4.