Sarkin Gobir na Gatawa, Alhaji Isa Muhammad Bawa da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da shi ya bukaci taimakon Gwamnatin Jihar Sakkwato, domin kubutar da shi daga hannunsu.
‘Yan ta’addan sun yi garkuwa da tsohon Sarkin Daular Gobir da ke Sabon- Birni tare da dansa kusan makonni uku a kwanar Maharba da ke a Goronyo a kan hanyarsa ta komawa gida Sabon- Birni daga Sakkwato, inda suka rika harbi ba kakkautawa wanda ya tilastawa motarsa tsayawa.
- Hadin Gasasshen Burodi Da Kwai Da Madara
- Shugabannin SADC Za Su Hallara A Sabon Ginin Ofishin Da Sin Ta Tallafa Wajen Ginawa Domin Gudanar Da Taron Shekara
‘Yan ta’adda na cin karensu ba babbaka a Gabascin Sakkwato da ke da kananan hukumomi shida, inda suke kisan gilla, garkuwa da mutane, satar shanu, mayar da garuruwa kufai da tilastawa al’umma kaurace wa gona.
Da farko ‘yan ta’addan sun bukaci a biya kudin fansar Sarkin Naira biliyan daya, amma daga baya suka rage kudin zuwa Naira miliyan 500.
A wani faifan bidiyon na minti daya da ‘yan ta’addan suka saki a ranar Asabar wanda aka dauka a ranar Laraba, an nuno Sarkin cikin daji a cikin mummunan yanayi da zubar jini a rigarsa yana cewar yana jin jiki kuma gwamnatin Sakkwato ba ta taimake shi ba.
“Ina rokon ‘yan uwana da masoyana da abokaina da shugabanni na cewar an kai rana ta karshe yau Laraba, don haka ina so su taimake ni. Ina sanar da su cewar wallahi, wallahi mutanen nan sun ma gaji da mu don duk abin da ake yi sun yi amma gwamnatinmu ba ta taimake ni ba, kuma ina ganin duk halin dana shiga a duniya za ta taimake ni amma ba ta taimake ni ba.”
“Ni ma’aikacin gwamnati ne shekara da shekaru ina bauta mata, na yi shekaru 45 ina bautawa gwamnati kuma duk a aikin sarauta.” cewar Sarkin wanda ba a nuno fuskar ‘yan bindigar da ke yi masa bidiyo da tambayoyi ba.
Sarkin na Gatawa ya rasa rawaninsa na babbar sarautar Sarkin Gobir na Sabon- Birni wadda ke da dadadden tarihi a watan Afrilu a yayin da gwamnatin Sakkwato ta tube rawanin Sarakuna 15 tare da sauyawa wasu masarautu.
An rage masa girma tare da mayar da shi Sarkin Gatawa, masarautar da ke karkashin ikonsa
Jim kadan da garkuwa da Sarkin, Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan, Ahmad Rufa’i, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da cewar suna kan gudanar da bincike kan lamarin.