Ƙasar Qatar ta fara wasan gasar Kofin duniya da ƙafar hagu bayan da ta sha kashi a hannun Ecuador da ci biyu da nema a filin wasa na Al Bayt.
BBC ta rawaito cewa, Enner Valencia ne ci duka kwallayen biyu kafin a je hutun rabin lokaci, bayan da na’urar taimaka wa alƙalin wasa ta VAR ta soke ƙwallon farko da ya ci.
- Gasar Kofin Kwallon Kafa 2022: Qatar Ta Haramta Hadadar Barasa A Filayen Wasanninta
- Gasar Kofin Duniya: An Gargadi ‘Yan Nijeriya Kan Bin Dokokin Kasar Qatar
‘Yan wasan Qatar sun shafe wata shida a sansani guda suna shirya wa gasar to amma duk da haka da alama haƙarsu ba ta cimma ruwa ba.
A yayin da zakarun Afirka wato Senegal da kuma Netherlands wadda sau uku tana zuwa wasan ƙarshe a gasar ke cikin rukuni guda da Qatar ɗin, an yi tunanin wannan wasan shi ne zai iya zama mai sauƙi ga ƙasar ta Qatar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp