“Wannan gasar wasanni ta Asiya ta kasance abin ban mamaki, wanda ba za a manta da shi ba, kuma ta cimma nasarar da ba a taba samu ba.” Da yammacin jiya Lahadi 8 ga watan Oktoban nan ne aka rufe gasar wasannin Asiya karo na 19 a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang na kasar Sin, kuma mukaddashin shugaban kwamitin wasannin Olympics na Asiya Raja Randhir Singh, ya yi wannan tsokaci ne yayin bikin rufe gasar.
A cikin kwanaki 16 da suka gabata, kasar Sin ta cika alkawarin da ta dauka, tare da gabatar wa duniya wata gagarumar gasar mai “halayen Sin, da salon Asiya, da kuma ban sha’awa”. Har ila yau, duniya ma ta samu kyakkyawar fahimta, game da kasar Sin ta hanyar wannan gasa mafi girma da aka yi a Asiya.
- Jiragen Kasa Dake Tafiye-Tafiye Kan Yankin Ciyayi Na Pampas
- Xi Ya Fadawa Schumer Yadda Sin Da Amurka Za Su Daidaita Zai Tabbatar Da Makomar Bil Adama
Bisa kokarin bangeren kasar Sin, gasar wasannin Asiya ta Hangzhou ta samu sakamako mai kyau, wanda ya karya matsayin bajintar tarihin duniya sau 15, da na tarihin Asiya sau 37, da kuma na tarihin gasar sau 170.
Daga cikin tawagogi 45 da suka halarci gasar, 27 sun samu lambobin zinare, yayin da 41 suka samu lambobin yabo. Gasar ta wannan karo ta kuma kasance wadda aka fi samun yawan lambobin yabo a duk wasannin Asiya da suka gabata.
Ta hanyar wannan dandalin wasannin Asiya na Hangzhou, mutane daga kasashe daban-daban sun tsallake bambance-bambance ta fuskokin yanki, launin fata, da al’adu don kulla abota mai zurfi. A matsayinta na gasar Asiya ta farko a tarihi da ta gabatar da manufar shirya wasannin ta hanyar “fasahar zamani”, wasannin Asiya na Hangzhou sun kuma baiwa duniya damar ganin kasar Sin ta zamani dake ci gaba da yin kirkire-kirkire.
Karfin zaman lafiya, da hadin kai, da hakuri da wasannin Asiya na Hangzhou ke kawowa zai haskaka Asiya, tare da inganta gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga yankin Asiya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)