A jiya Alhamis ne aka kaddamar da gasar wasanni ta mutum mutumin inji ta duniya a birnin Beijing na kasar Sin, wadda ke gabatar da sabbin ci gaban da aka samu a bangaren aiki da basira da motsi, wajen kera mutum mutumin inji.
Kungiyoyi 280 daga kasashe 16, ciki har da Amurka, da Jamus, da Italia ne za su fafata a gasar da za a yi daga Juma’a zuwa Lahadi, a dakin wasan gudun kankara na kasa. Mutum mutumin injin za su fafata ne cikin wasanni 26 na motsa jiki, kamar gudu, da dogon tsalle, da sarrafa jiki, da kwallon kafa, da ma wasu ayyukan da suka shafi basira a fannoni daban-daban kamar jigilar kayayyaki, da ware magunguna, da aikin tsafta.
A cewar Li Yechuan na ofishin kula da harkokin tattalin arziki da fasahar sadarwa na birnin Beijing, gasar ta yi amfani da wasannin bil adama ne domin gwada sabbin ci gaba da aka samu a basirar mutum mutumin inji. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp