Kwanan nan ne wani mummunan bala’i ya wakana a jihar Texas dake kasar Amurka, inda aka gano wata babbar mota da aka yi watsi da ita a birnin San Antonio dake jihar, wadda ke cike da gawarwakin bakin haure masu tarin yawa. Kawo yanzu yawan mamatan ya karu zuwa 51, al’amarin da ya zama daya daga cikin bala’un mutuwar bakin haure mafi muni a tarihin Amurka.
Wannan ba shi ne karo na farko da aka samu irin wannan masifa ba a Amurka. Me ya sa Amurka ta gaza wajen daidaita matsalar bakin haure? Daya daga cikin muhimman dalilai shi ne, rikicin jam’iyyun siyasa.
Za’a gudanar da zaben rabin zango a Amurka, inda batun bakin haure ya sake kasancewa tamkar abun sa-in-sa tsakanin manyan jam’iyyun siyasar kasar. Kamar yadda Mujallar Siyasa ta Amurka ta ce, batun bakin haure siyasa ce kawai, wadda ‘yan siyasar kasar ke amfani da ita don cimma burinsu.
Tun farkon hawan sa karagar mulkin Amurka, Joe Biden ya yi alkawarin kawo sauyi ga shirin doka, kan masu kaura daga dukkan fannoni, amma har yanzu ba’a samu ci gaba ba.
Manazarta na ganin cewa, matsanancin talauci, da munanan laifuffukan da ake aikatawa, suna zama muhimman dalilan da ke sa mutane kokarin ficewa daga yankin Latin Amurka.
Wani masanin batutuwan masu kaura daga kasar Salvador, Cesar Rios, ya ce, Amurka ta dade tana ikirarin cewa wai tana da niyyar daidaita matsalar bakin haure tun daga tushe, amma har yanzu kasashen yankin tsakiyar nahiyar Amurka, ba su ga matakan zahiri da Amurka ta dauka ba.
Idan da gaske ne ‘yan siyasar Amurka na maida hankali kan al’ummar Latin Amurka, to, kamata ya yi su dauki kwararan matakai na kare hakkin bakin haure, da na ‘yan gudun hijira, a wani kokari na hana faruwar irin wannan masifar jin kai. (Murtala Zhang)