Yau Juma’a, hukumar kididdiga ta kasar Sin ta ba da alkaluma dake cewa, yawan karfin tattalin arzikin kasar Sin a ma’aunin GDP a shekarar 2024, ya kai fiye da dalar Amurka tiriliyan 18.4, adadin da ya karu da kashi 5% bisa na makamancin shekarar 2023.
Sin ta samu irin wannan nasara ce duk da karuwar matsin lamba daga waje, da wahalhalu daga gida, inda a karon farko yawan GDPn kasar ya zarce kimanin dala triliyan 17.7, kana ta ci gaba da zaune a matsayi na 2 a duniya a wannan bangare ba tare da tangarda ba.
Idan mun duba a duk fadin duniya, saurin bunkasuwar tattalin arzikin Sin da yawansa ya kai 5%, yana ci gaba da zama a matsayin muhimmin karfin gaggauta bunkasuwar tattalin arzikin duniya. (Amina Xu)