A yayin da shugaba Bola Tinubu ya sanar da nada Dakta Abubakar Dantsoho a matsayin Manajin Daraktan Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, a ranar 12 ga watan Yulin 2024, masu ruwa da tsaki suka fara yakinin cewar, fannin zai kara tunbatsa maye da yadda yake a baya.
Sai dai, tunain na samun sauki ga fannin ba wai domin Dantsoho ya shafe shekaru yana da kwarewa a fannin bane.
- Bajintar Aiki: Majalisar Dattawa Ta Jinjina Wa Ministan Yaɗa Labarai
- Hisbah Ta Yi Kakkausan Gargaɗi Tare Da Kira Ga Iyaye Kan Kula Da Yara Bayan Samun Gawar Wasu 4
Kusan masu ruwa da tsaki a fannin da ke a lungu da sako na kasar nan, an yi maraba da dadin na Dantsoho, domin sun yi ammmanar cewa, nadinsa, abu ne da ka yi yadda ya dace.
Duba da shekaru 25 da na kwarewa da Dantsoho yake da su a fannin, ya faro aikinsa ne, tun a 1992, a yayin da ya yiwa kasa hidima na shekara daya a wato NYSC, a Hukumar
Kazalika, kasancewar yana da kwarewa a fannin fasahar kimiyyar harkokin ruwa da kuma ta samar da fasfot din tafiye-tafiyen na kasa da kasa, hakan ya kara sanyawa, masu ruwa da tsaki a fannin, sun kara aminta da shi.
Duba da irin wannan kwarewar da Dantsoho yake da su, babu wata tantama, zai kara samar da dimbin nasarori a fannin a 2025.
Wasu daga cikin jeren nasarorin da ake sa ran zai samar sune, zamanantar da Tashoshin Jiragen Ruwa na kasar, sake sabunta jarjejeniyar zuba hannun jari da kuma gyran kayan da ake aiki da su, a Tashoshin Jiregen Ruwan kasar da sauransu.
A lokacin da ya kama aiki, matsayin sabon Manajin Daraktan Hukumar, Dantsoho ya yi alkawarin saita Tashohin Jiragen Ruwa na kasar, musamman don ci gaba da bayar da gudunmwarsu, wajen kara habaka tattalin arzikin Nijeriya.
Domin ya tabbatar da wannan alkwarin na sa, tuni dai, Dantsoho, ya kaddamar da nufin bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa na kasar.
Bugu da kari, sa ran da ake yi idan aka saita Tashohin Jiragen Ruwan kasar, hakan zai dora kimasu, a kan gaba a yankin Afrika ta Tsakiya, tare da kuma ture karbe tarhin da Tashar Jiragen Ruwa ta Abidjan, ke da ita.
Mayar Da Tashar Zuwa Ta Zamani:
Hukumar ta NPA, ta yi namijin kokari wajen wajen mayar da Tashar zuwa ta zamani, tare da kuma daga darajar kayan da ake amfani da su, a Tashar, misali rage cunkso a kofar shiga Tashar da ke a Apapa.
A watan Yulin 2024, Hukumar kaddamar da aikin yin amfani da na’urar zamani a Tashar da ke Onne Port, wanda hakan ya sanya aka samu kashi 25, na karin kayan da ake saukewa a ajewa a Tasahar.
Sake Gyran Gurin Sauke Kaya Da Ke A Tashar:
A watannin baya, Gwamnatin Tarayya ta nuna bacin ranta kan yadda yanayin wajen sauke kaya ya kaance da ke a Tashar Tin-Can Island da ke a Jihar Legas.
Hakan ya sanya a Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, a watan Janairun 2024, ya umarci Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje da ta gaggauta gyra wajen, musamman domin a samar hanyoyi, ciki har da gyran ta wajen kaya na Tin-Can Island da ke a Legas.