Alkaluman hukumar kididdaga ta kasar (NBS) sun nuna a yau Litinin cewa, yawan GDPn kasar Sin ya karu da kashi 5 cikin dari a farkon rabin shekarar 2024, idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara.
GDPn kasar Sin ya kai kusan Yuan tiriliyan 61.68 kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 8.65 a farkon rabin shekarar kamar yadda alkaluman NBS suka nuna.
- An Kaddamar Da Zama Na 3 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20
- Sufeta Janar Na Ƙasa Ya Dakatar Da Aiwatar Da Na’urar E-CMR Bayan Shan Suka
Kudin shiga na kowane mutum bayan haraji na kasar Sin a farkon rabin shekarar ya kai Yuan 20,733 kwatankwacin dalar Amurka 2,907.32, wanda ya karu da kashi 5.4 cikin dari bisa na shekarar da ta gabata.
Yawan sayayyar kayayyakin masarufi na kasar Sin ya karu da kashi 3.7 cikin dari a farkon rabin shekarar bana bisa makamancin lokacin bara.
Yawan iskar gas da kasar Sin ta samar ya ci gaba da habaka, kasar ta samar da iskar gas cubic mita biliyan 123.6 a tsakanin watan Janairu zuwa Yuni, wanda ya karu da kashi 6 cikin dari idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata. (Mai fassara: Yahaya)